1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan takara fiye da 50 na kalubalantar sakamakon zaben 2023

Muhammad Bello RGB
April 4, 2023

Yan takara da suka sha kaye a zaben Najeriya na 2023, na shirin shigar da kara a gaban kotu domin kalubalantar sakamakon da Hukumar INEC ta fitar.

https://p.dw.com/p/4PgMC
Zanga-zangar kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar Najeriya
Zanga-zangar kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar NajeriyaHoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto/IMAGO

Hankulan 'yan siyasa da suka yi takara mukamai daban-daban a zabukan da su ka gabata na Najeriyar, kuma ba su kai ga nasara ba, sun koma kan batun tunkarar kotunan sauraren kararrakin na zabe da hukumar zabe ta kasa ta kafa.

Ko da ya ke tun bayan gudanar da zabubbukan na Najeriyar, wadanda musamman ba su kai ga nasarar ba, ke ta kokarin ganin hukumar ta zabe ta ba su damar, dudduba naurori da hukumar ta yi amfani da su yayin zabukan da kuma wasu mahimman takardu da ke dauke da bayanan ma su kada kuriu da ma adadin kuriun kansu.

Dan takarar shugaban kasa Peter Obi
Dan takarar shugaban kasa Peter ObiHoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto/picture alliance

Wasu 'yan siyasar, sun samu damar hakan, in da wasu kamar jam'iyyar APC a jahar Rivers ke ci gaba da fuskantar matsalar zanga-zanga mara dalili ta 'yan siyasa, kamar yadda jam'iyyar APC ta zarga, cikas ne gare ta kan tattara bayanan tunkarar kotun zabe.

Yan takara akalla 13 na kalubalantar sakamakon zaben jihar Rivers
Yan takara akalla 13 na kalubalantar sakamakon zaben jihar RiversHoto: Getty Images/AFP/U. Ekpei

Yayin da jihar Cross River ke da koke-koke akalla 13, jihar Akwa Ibom kuma 15 gare su, da su ka hada da 'yan majalisun tarayya 11, 4 kuma na 'yan majalisar dattijai, duka da su ka sha kaye, a jihar Bayelsa kuwa, duka koke-koke 9 kan zaben kujerar 'yan majalisun tarayya ne.

Babban batu da ma shi ne dai ya fi daukar hankula, shi ne na kalubalantar zaben kujerar shugaban kasa da jam'iyyun Labour da PDP musamman ke ci gaba da yi , da kuma ke shirin tsaf na bin bahasi a gaban wannan kotu ta sauraren kararrakin zabe.

Wadanda su ka sha kaye a zaben Najeriyar, na da kwanaki 21 ne kacal bayan zabe, na su kalubalanci sakamakon zaben, a bisa dokar zabe ta shekarar 2022. Kungiyoyi da dama na ta kirayen ganin Hukumar ta zabe ta hanzarta sauraren wadannan korafe-korafe cikin hanzari.