1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kano: Kotu ta tabbatar da Gawuna maimakon Abba

Nasir Salisu Zango AH
September 20, 2023

Kotun ta tabbatar Dr. Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin sabon gwamnan Kano, bayan zartas da hukunci a kan shari'a kan karar zaben da ya gudana a watan Maris 2023

https://p.dw.com/p/4WbDj
Abba Kabir Yusuf  da Dr. Nasiru Yusuf Gawuna
Abba Kabir Yusuf da Dr. Nasiru Yusuf GawunaHoto: Private/Bashir Ahmad/Facebook

Kotun sauran kararrakin zabe ta tabbatar  Dr. Nasiru Yusuf Gawuna na APC a matsayin gwamnan Kano a gaban Abba Kabir Yusif na NNPP. Bayyana wannan sakamako ya biyo bayan watannin bakwai da gudanar da zabubukan gama gari a Najeriya.Tun bayan bayyana hukuncin kotun sauraran kararrakin zabe ta Jihar Kano da ta tabbatar da Dr Nasiru Yusif Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben 2023 da aka yi tare da soke zaben gwamna me ci Engr Abba Kabir Yusif mutane suka bazama a sassan jihar dabam-dabam inda wasu ke murna wasu kuwa na bakin cikin matakin kotun. yanzu haka dai wasu matasa sun fara yin kone kone da nufin nuna kin amincewar su da hukunci

 Kotu ta amince da korafin jam'iyyar APC 

Nigeria Blasphemie Prozess
Hoto: REUTERS

Tun da misalin karfe 10 saura mintuna kadan ne,aka fara zaman kotun sai dai  wani shammace da alkalan kotun suka yi shi ne maimakon agan su a zahiri sai suka bayyana a allon manhajar majigin zamani da akewa lakabi da zoom, alakan uku ne sun kuma saka shugabar su Justice Osadabe a tsakiya ita ce ma tayi dogon karatu na kimanin awanni fiye da biyar kafin daga karshe ta bayyana cewar bisa hujjoji da suka bayyana gabanta,ta amince da korafin jam'iyyar APC na kalubalantar sakamakon zaben dan haka ta soke zaben da aka yi wa Engr Abba Kabir Yusif ta kuma ayyana Dr Nasiru Yusif Gawuna na jamiyyar APC a matsayin halastaccen wanda ya lashe wannan zabe, to amma a ra’ayin lauyoyin jam'iyyar NNPPwannan hukuncin surkulle ne wanda hankali ba zai dauka ba amma ya ce za su runtuma gaba domin daukaka kara.