1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddamar zabe ta kai kotun koli

Suleiman Babayo AMA
September 19, 2023

Manyan 'yan takara biyu a zaben Najeriya sun kalubalanci sahihancin zaben shugaban kasar a gaban kotun kolin kasar.

https://p.dw.com/p/4WZY4
Bildkombo Nigeria Wahlen | Peter Obi, Bola Tinubu (M), Atiku Abubakar
Hoto: K. Gänsler/DW, Shengolpixs/IMAGO, EKPEI/AFP

Manyan 'yan takara guda biyu na neman shugabancin Najeriya a zaben da ya gabata sun kalubalanci sahihancin sakamakon zaben da aka yi wa Shugaba Bola Tinubu a gaban kotun kolin kasar da ke birnin Abuja fadar gwamnatin.

'Yan takaran biyu Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da ya zo na biyu a zaben da Peter Obi na jam'iyyar Labour, kowanne ya shigar da kara, bayan tun farko kotun sauraron kararrakin zabe ta tabbatar da sahihancin zaben na watan Febrairu.

Tun lokacin da Najeriya ta koma tafarkin dimukaraddiya a shekarar 1999 kimanin shekaru 24 da suka gabata babu wanda ya yi nasarar ganin soke sakamakon zaben shugaban kasa, a kasar mafi yawan mutane tsakanin kasashen nahiyar Afirka.