1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa ta harba wani makami mai linzami

Abdourahamane Hassane
December 18, 2023

Koriya ta Arewa ta harba wani makami mai linzami mai cin dogon zango da ka iya kai wa Amurka, kamar yadda Koriya ta Kudu da Japan suka sanar.

https://p.dw.com/p/4aHQk
Hoto: Korean Central News Agency/AP/picture alliance

 Wadannan hare-hare guda biyu a jere sun zo ne 'yan kwanaki bayan gargadi daga Seoul da Washington wadanda suka gargadi Koriyar ta Arewan cewa duk wani harin nukiliya kan Amurka ko kawayenta zai kawo karshen mulkin Kim Jong Un, shugaban Koriya ta Arewan. Rundunar sojin Koriya ta Kudu ta sanar da cewa, ta gano harbin makami mai linzami mai cin dogon zango da aka harba daga yankin Pyongyang, inda ta yi kiyasin cewa ya yi tafiyar kilomita dubu kafin ya fada tekun Japan.