1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

Kim Jong Un na ci gaba da ziyara a Rasha

September 16, 2023

A ci gaba da ziyarar da yake, shugaban Koriya ta Arewa ya isa birnin Vladivostok da ke Arewa mai nisa ta kasar Rasha inda ya samu kyakkyawan tarbe daga ministan tsaro Sergei Shoigu.

https://p.dw.com/p/4WPok
Kim Jong Un ya isa birnin Vladivostok na RashaHoto: Russian Defense Ministry Press Service/AP/picture alliance

Dama a lokacin da ya gana da takwaransa Vladimir Putin shugaban ya sanar da cewa Kim Jong Un zai halarci wani kasaitaccen atisayen jiragen ruwan yaki da za a gudanar a tekun Pacific.

Karin bayani: Shugaba Kim ya gana da Putin

Tuni dai kasashen Yamma ciki har da Amurka suka fara martani kan ziyarar, suna masu zargin Moscow da neman cefano makamai daga Piyongyang domin kara karfin sojojinta da ke daga a Ukraine, yayin da ita kuwa Koriya ta Arewa ke neman mallakar fasahohin zamani domin ingata shirinta na Nukiliya da kera makamai masu linzami.

Karin bayani: Ziyarar Kim ga Putin ta sa Amurka fargaba

A yayin ziyarar da ya fara a ranar Talata (12.09.2023) wacce ke zama ta farko tun bayan barkewar annobar Covid-19, shugaba Kim Jong Un ya gayyaci takwaransa Putin zuwa Koriya ta Arewa, sai dai ba bu wata matsaya a hukumance da shugabannin biyu suka cimma a cewar kakakin gwamnatin Rasha Dmitry Peskov.