1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar NPP ta karbi wani wa'adin mulki a Ghana

December 10, 2020

Ghana ta ciri tuta ta hanyar kare martabartar dimukuradiyya, bayan gudanar da zabe cikin tsanaki da kwanciyar hankali ba tare da wani kone-kone ko kashe-kashen jama'a ba.

https://p.dw.com/p/3mXcH
Afrika Ghana Präsidentschaftswahlen
Yadda wani dan kasar Ghana ke kada kuri'a a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisaHoto: Ofoe Amegavie/AP/picture alliance

A matsayin na na dan kasar Ghana shakka babu zan yi alfahari da kyawon sunan da kasa ta tayi na kasancewa mai sahihiyar mulki dimokuradiyya, amma hakan bai ratsa zuciyata ba, don a gareni shugabanci na gari ya zarta burgar gudanar da sahihin zabe cikin kwanciyar hankali da babu kashe-kashe da kone-kone, wannan ba shi kadai bane ci gaba misali idan ana zabe a Jamus, babu batun fargabar rikici hakazalika a Britaniya da Faransa da sauransu babu gardama a mika mulki duk da cewa Shugaba Donald Trump na Amirka ya kafa munmunan tarihi a siyasar kasar bisa nuna tirjjiya kan sakamakon zaben kasar, amma babu rikici ko asarar rai ko fyade da gallazawa bangaren adawa, saboda haka mai zai sa a dauki gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali a Afrika ya kasance wani ci gaba? Abun tambaya shi ne wasu lamura da suka auku a zaben da ake alfahari da shi, yana ma da wuya a iya ware zare da abawa don kuwa manyan jam'iyyun biyu NDC da NPP duk daya suke bambancinsu suna da adawa da juna ne kawai.

NDC da NPP sun yi mulki na tsawon shekaru

Kombibild Ghana Nana Akufo-Addo und John Dramani Mahama
Nana Akufo-Addo da John Dramani Mahama

Matsalar siyasar Ghana kenan wadannan jam'iyyun biyu ne ke shugabanci tun daga shekarrar 1992 da kasar ta koma tafarkin mulkin dimokuradiyya, da wannan nasarar ta jam'iyyar shugaba Nana Akufo Addo,  yana nufin jam'iyyun kowanne su ya ci zabe sau hudu, kuma ba wai jam'iyyun kadai ba, a'a mulkin ya dawammam a hannu Shugaba Nana Akufo Addo da Tsohon shugaba John Mahama Dramani da wannan ne karawarsu ta uku a zaben shugaban kasar baya ga Shugaba John Evans Atta Mills da ya mutu a karagar mulki a shekarra 2012.

Karin Bayani: Al'ummar Ghana na dakon sakamakon zabe

Duk wannan na nufin dimokradiyar Ghana ta ki girma don har yanzu rarrafe take, a takaice lamurra na sake tabarbarewa, shekaru goma da suka gabata bana fargabar gudanar da aiki na na jarida a kasar amma yanzu labarin ya sha bambam duk inda zani sai da rakiyar jamai'an tsaro  saboda barazanar da rayuwa ke fuskanta, bani kadai ba akwai dan jarida  mai binciken kwakwaf Ahmed Hussein-Suale, da aka harbe har lahira bayan barazana daga wani dan jam'iyyar shugaba Akufo-Addo.

Karin Bayani: Tarihin Nana Akufo-Addo zababben shugaban Ghana

Lashe zabe ba tare da wani sauyi ba a Ghana

Ghana Wahlkampf
Nana Akufo-Addo na yakin neman zabeHoto: Reuters

A takaice ma dai babu alamar da za ta nuna min cewa za a ga sauyi daga yanzu zuwa zaben 2024, don kuwa kamar sauran kasashen nahiyar Afrika cin hanci da barnata dukiyar gwamnati sun kasance karfen kafa a hana ci gaban Ghana Shugaba  Akufo-Addo ya lashe zaben 2016 bisa alkawarin magance matsalar cin hanci da rashawa da ta yi wa gwamnatin Shugaba John Mahama na wancan lokaci katutu.

Karin Bayani: Yarjejeniyar zaman lafiya kafin zabe

Sai ga shi jiya zuwa yau, shi ne ma ya kasance babban kalubalensa a wannan zabe wanda da kyar ya kai labari. Baya ga haka sanin kowa ne gwamnatin Akufo-Addo's ta ranci kudi a wa'adin mulkin farko kudin da suka zarta duk adadin bashin da Ghana ta ci tun bayan samun 'yancin kai. Amma duk da haka ba zan soki al'ummar Ghana ba bisa alfaharin da suke yi da kasar ai dama masu iya magana na cewa a duniyar makafi mai ido guda sarki ne.

Duk da haka ina cike da fata nagari zan iya yin alfahari da kasa ta muddun Shugaba Akufo-Addo yayi amfani da wa'adin mulkinsa na biyu a inganta rayuwar jama'a da gina kasa, ya guji shugabanci na yan uwa da abokan arziki ya zage damtse ya yaki cin hanci, in har yai nasara, to nan ne zan iya taku na kasaita in yi alfahari da kasa ta a matsayin wacce ta yi zarra a iya gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali a nahiyar Afrika.