1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaBurundi

An cika shekaru 30 da kawo karshen yakin basasar Burundi

Schwikowski Martina AH
October 21, 2023

An cika shekaru 30 da kawo karshen yakin basasar da aka yi a Burundi bayan cimma yarjejeniyar zaman lafiya a birnin Arusha na Tanzaniya a shekarun 2000.

https://p.dw.com/p/4Xr6D
Burundi Massaker Genozid 1972
Hoto: YASUYOSHI CHIBA/AFP/Getty Images

An zabi Melchior Ndadaye, a ranar daya ga watan Yunin na shekara ta 1993 bayan zaben dimokaradiyya na farko a kasar tun bayan samun 'yancin kai daga kasar Beljiyam. A shekara ta 1962, al hakika wasu tsirarun sojojin Tutsi ne ke mulkin Burundi. Bayan an kashe Nadadaye Brundi ta fada cikin yakin basasa tsakanin sojojin da 'yan kabilar Tutsi suka mamaye da kuma kungiyoyin 'yan tawayen Hutu, inda aka kashe mutane fiye da dubu 300, yayin da dubban darurruwan mutane suka tsere zuwa kasashe makwabta.Sylvestre Ntibantunganya tsohon shugaban Burindi ne kuma ya ce kisan na Nadadaye ya janyo muguwar kiyayya da gaba a tsakanin al'ummomin Burindi: ''Wannan kisa na Ndadaye ya haifar da kiyayya a tsakanin 'yan Burundi, inda suka bijire wa juna, abin da ya janyo kazamin yaki a tsakaninsu sama da shekaru 10. Kasar ta koma baya ta fuskar tattalin arziki. Ni da kaina ina ganin Burundi ta yi babban rashi a wancan lokacin saboda  Melchior Ndadaye mutum ne da ya kuduri aniyar yaki da matsanancin talauci a Burundi, kuma yana da kwakkwaran tsare-tsare don cimma hakan, da kuma ganin  'yan Burundi su zauna tare cikin lumana."

Sulhun da ya kawo karshen yakin Burundi a yarjejeniyar Arusha

Burundi Massaker Genozid 1972
Hoto: ONESPHORE NIBIGIRA/AFP/Getty Images

A shekarun 2000 aka kawo karshe yakin na Burundi bayan cimma yarjejeniyar zaman lafiya a birnin Arusha na Tanzuaniya, sai dai yakin ya haifar da munanan raunuka. Yarjejeniyar zaman lafiya ta kafa harsashin raba madafun iko tsakanin kabilun biyu a dukkan matakai a gwamnati, da majalisa, gudanarwa, da 'yan sanda da sojoji. An sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta a shekara ta 2003. Sylvestre Ntibantunganya ya ce an koyi darasi: "Darasi na farko shi ne cewa a yanzu da dama daga cikin 'yan Burundi sun fahimci cewa babu wata hanyar da ta wuce neman yardar al'ummar kasar ta hanyar zabe mai cike da gaskiya da adalci. Darasi na biyu shi ne cewa a yanzu 'yan Burundi sun fahimci mahimmancin tsarin jam'iyyun siyasa da dama, kuma rawar da kungiyoyi masu zaman kansu da kafafen yada labarai suke takawa wajen tabbatar da dimokaradiyya da inganta hakkin dan Adam. Amma babban darasi shi ne cewa a halin yanzu 'yan Burundi sun san mahimmancin tattaunawa yayin da matsaloli suka taso a tsakaninsu."

Al'ummar Burundi na ganin mahimmancin tattaunawa don warware rikici

Bürgerkrieg Ruanda Afrika Tutsie Burundi Zaire
Hoto: afp/picture-alliance

Bayan murkushe masu zanga-zangar adawa da wa'adin mulki na uku a shekara ta 2015 mai cike da cece-kuce na shugaban kasar na wancan lokacin Pierre Nkurunziza, Burundi ta kasance saniyar ware a duniya na tsawon lokaci, sannan an danne 'yan adawa da kungiyoyin fararen hula.Tare da shugaban kasar na yanzu, Evariste Ndayishimiye, wanda ke kan karagar mulki tun shekarar ta 2020, manufofin harkokin wajen kasar sun kara karfafa, amma har yanzu bai yi wani gagarumin sauyi ba a cikin gida.