1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Barazanar tsaro ga makarantu

March 11, 2024

Jihohi 14 daga cikin 36 na Najeriya na fuskantar barazanar tsaro a makarantu, lmarin da ke nuna irin matsalolin tsaro da suka mamaye kasar mafi yawan jama'a tsakanin kasashen nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/4dOiF
Makarantar da aka sace dalibai a Najeriya
Makarantar da aka sace dalibai a NajeriyaHoto: AP/dpa/picture alliance

A wani abun da ke kara fitowa fili da girman rikici na ceton dalibai cikin makarantun Najeriya, makarantu a akalla iihohi 14 ne fuskantar barazanar mai hatsari ga makomar ilimi. Ya zuwa yanzu dai sama da dalibai 400 na hannun dillallan zubar da jinin da ke a dazuka maimakon azuzuwa na neman ilimi. Adadin kuma da ke iya karuwa sakamakon karuwar barazana da dalibai cikin makarantu ke fuskanta.

Karin Bayani: Kaduna: Ko daliban da aka sace za su tsira?

Garin da aka sace dalibai a Najeriya
Garin da aka sace dalibai a NajeriyaHoto: AP/dpa/picture alliance

Shirin kare makarantu na kasar dai ya ce makarantu a jihohin arewacin kasar kimanin 14 dai na neman taimaka shirin da nufin kaucewa barazanar da kan tilastawa dalibai barin aji. Ya zuwa watan Disamban da ya shude dai sama da kaso 50 cikin Dari na yara miliyan 10.5 da ba sa makaranta a cikin Najeriya sun fito ne daga sashen arewacin kasar. Sashen da ke zaman na baya ga dangi ga batun ilimi, Sannan kuma mattatara rashin tsaron kasar. Akwai dai tsoron karuwar koma-baya cikin batun ilimin yara a Arewa a fadar Abdul Ghaniyu Abubakar dake jagorantar kungiyar "Save the child" mai fafutukar ingantar ilimi a arewacin kasar.

A baya dai Najeriya ta kashe dubban miliyoyi na daloli a kokari samar da tsaro a cikin makarantu da ma cikin gari. To sai dai kuma tana shirin karewa da ta'azzarar rashin tsaron a daukacin arewacin kasar. Kabir Adamu na zaman shugaba na kamfanin Beacon Consult da ke nazari nisa batun tsaron. Kuma ya ce sashen arewacin kasar bashi da sabi face zama wuri guda domin tunkarar lamarin.