1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

An gano gawarwaki kusan 200 a asibitin Gaza

April 22, 2024

Hukumomi a Gaza na Falasdinu, sun ce a cikin kwanaki uku da suka gabata ma'aikatan kiwon lafiya sun gano kusan gawarwaki 200 na mutanen da sojojin Isra'ila suka kashe kuma suka binne a asibitin Khan Yunis.

https://p.dw.com/p/4f4Jx
Birnin Khan Yunis na Gaza
Birnin Khan Yunis na GazaHoto: Ali Jadallah/Anadolu/picture alliance

Sojin Isra'ila dai ba su ce uffan ba a kan wannan batun ya zuwa yanzu.

Mai magana da yawun hukumar Mahmud Bassal ya ce akasarin gawarwakin sun rube kuma akwai wahalar gane su saboda irin yanayi da suke ciki, amma hukumar tana iya kokarinta.

Da yake karin haske kan lamarin, shugaban ofishin yada labarai na gwamnatin Hamas a yankin na Zirin Gaza Ismail Al-Thawabta ya ce gawarwakin mutane 283 aka gano a asibitin.