1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Harin Isra'ila ya kashe jami'an agaji 7 'yan kasashen waje

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
April 2, 2024

Sauran wadanda suka mutu sun fito ne daga kasashen Burtaniya da Amurka da Poland, sai Canada da kuma direbansu Bafalasdine

https://p.dw.com/p/4eKCx
Hoto: Abdel Kareem Hana/AP Photo/picture alliance

Jami'an agajin wata kungiyar kasar Spain 7 ne suka mutu, sanadiyyar harin da Isra'ila ta kai wa motarsu a garin Deir al-Balah na Zirin Gaza ranar Litinin, kamar yadda kungiyar da suke yi wa aiki ta World Central Kitchen wato WCK ta wallafa a shafinta na X.

Karin bayani:Paparoma Francis ya yi kiran a tsagaita wuta a Zirin Gaza

Firaministan Australia Anthony Albanese ya shaida cewa daya daga cikin 'yan agajin 'yar kasarsa ce da ta yi fice wajen aikin jin kai, inda ya yi fatan ganin an kawo karshen yakin baki-daya.

Karin bayani:Gaza: Isra'ila ta zafafa kai hare-hare

Sauran wadanda suka mutu sun fito ne daga kasashen Burtaniya da Amurka da Poland, sai Canada da kuma direbansu Bafalasdine.