1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
LafiyaAfirka

Martani kan rigakafin cutar maleriya

October 7, 2021

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta amince da alluar rigakafin cutar zazzabin cizon sauro na farko a nahiyar Afirka inda masana harkokin kiwon lafiya suka nuna gamsuwa.

https://p.dw.com/p/41Otm
Gabun - Untersuchung in Malaria Studie
Hoto: Universität Tübingen/Christoph Jäckle

 

Cutar zazzabin cizon sauro ta kasance mai yawan yin barna tsakanin mutanen nahiyar Afirka inda a duk shekara dubun-dubatar mutane musamman yara na rasa rayukansu sanadiyyar wannan cuta yayin da miliyoyin kudi da ake kashewa na neman maganin don warkewa daga cutar.

Sanarwar da hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya wato WHO ta fitar na amincewa da allurar rigakafin cutar zazzabin cizon sauru da za a fara amfanin da shi a nahiyar Afirka ya farantawa da dama daga cikin masu yaki zazzabin cizon sauro da ma mutane da ke shan azaba daga illar da cutar ke yi tsakanin al'umma.

Medizin Forschung l Weltweit erste Malaria-Impfkampagne l Moskitonetz
Hoto: picture alliance/dpa/E. Morrison

Da yawa dai sun bayyana cewa samun wanan allurar rigakafi a wannan lokaci na da fa'ida kuma za ta taimaka gaya wajen yaki da cutar musamman tsakanin yara.

A cewar Sama'ila Idris Hinna jami'in kiowon lafiya a Najeriya duk da cewa samun wannan allura a wannan lokaci alheri ya kamata masana a kasashen nahiyar Afirka su kara yin gwaje-gwajen wannan allurar don tabbatar da sahihancin ta.

Karin Bayani: An samu allurar riga-kafin maleriya

Malama Badiya Sani wata uwa ce kuma mai yaki da cutar zazzabin cizon sauro a Arewa maso gabashin Najeriya , acewar ta da samun wannan allura za a samu raguwar mace-mace daga wannan cuta musamman tsaknain yara.

Malaria Impfung Afrika Kenia
Hoto: AP

Sai dai babban abin da mutane suka fi damuwa da shi shine wadatuwar da saukin allurar rigakafin  ta yadda ko mai karamin karfi da al'ummar da ke karkara za su samu ba tare da wata matsala ba. Amma ga Malam Ibrahim Gwamna Msheliza wani mai fashin baki kan harkokin yau da kullum bai kamata kuma a saki jiki don an samun wannan allurar rigakafin ba.

To sai dai akwai masu fashin baki da ke ganin matukar ba an yaki wanzuwar sauro ba akwai sauran a yaki da cutar abin da ya sa su karfafa kira ga hukumomi da su yaki sauro maimakon samar da magunguna ko rigakafin.