1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kawo karshen maleriya a Afirka

Wright, Louisa MNA
April 27, 2021

A duk shekara daruruwa dubbai na yara ne ke mutuwa sakamakon zazzabin cizon. Sai dai yanzu wata allurar riga-kafin maleriya da aka yi gwajinta a Afirka ta ba da sakamako mai karfafa gwiwa.

https://p.dw.com/p/3sdoe
Medizin Forschung l Weltweit erste Malaria-Impfkampagne l Impfstoff
Hoto: picture alliance/dpa/K.-J. Hildenbrand

Sama da mutane dubu 400 zazzabin cizon sauro ya yi ajalinsu a shekarar 2019. Sakamakon sabuwar allurar riga-kafin da aka wallafa a mujallar kimiyya ta The Lancet, kuma yanzu haka ake jiran a sake yin bincike kanta, ya nuna cewa riga-kafin samfurin R21/Matrix-M na da ingancin kashi 77 cikin 100, bayan an shafe wata 12 ana gwajinsa. Hakan ya dace da mizanin Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, cewa ingancin riga-kafin maleriya ya haura kashi 75 cikin 100. Yara 450 masu watanni haihuwa daga 5 zuwa 17, aka yi musu gwajin riga-kafin kuma ba a ga wani zazzabi mai tsanani a kan su ba. Yanzu haka dai masu binciken sun kara yawan wadanda za a yi wa riga-kafin don tabbatar da fa'ida da ingancinsa a kan yara 4800 daga watan haihuwa 5 zuwa 36. a kasashe hudu na Afirka. Julian Rayner mai bincike ne kan maleriya kuma daraktan cibiyar binciken kimiyya a jami'ar Cambridge da ke Birtaniya, ya bayyana sakamakon da abin karfafa gwiwa.Ya ce: "Abu ne mai karfafa gwiwa sosai da kuma ke tuni cewa maleriya babbar matsala ce da ke tare da mu, tana kuma bukatar sabbin maslahohi cikin gaggawa. Gwaji ne da ke a matakin farko, bayanan sun gamsar ko da yake yara kadan ne aka yi wa riga-kafin, amma ya ba mu kwari gwiwa na mu fadada shi."

Maleriya na haddasa mummunan kisa a nahiyar Afirka

Gabun - Untersuchung in Malaria Studie
Hoto: Universität Tübingen/Christoph Jäckle

Zazzabin cizon sauron dai cuta ce mai barazana ga rayukan mutane wanda macen sauro ke yada kwayoyinta bayan ta ciji mutum. Hukumar WHO ta yi kiyasin cewa a 2019 muatne miliyan 229 suka kamu da maleriya a fadin duniya, musamman a nahiyar Afirka inda aka yi rajistar kashi 94 cikin 100 na cutar da kuma wadanda ta yi ajalinsu a 2019. Yara 'yan kasa da shekara biyar ke da kashi 67 cikin 100 na wadanda maleriya ke sanadin mutuwarsu a fadin duniya. Sai Julian Ryaner na jami'ar Cambridge ya ce mutane da ke zaune a wuraren da aka fi fama malerya kuma suke yawan kamuwa da ita, jikinsu kan sama musu wata garkuwa.Ya ce: "Wannan ba cikakkiyar garkuwa ba ce ga cutar, ba ya nufin ba saka sake kamuwa da ita ba, amma zazzabin ba zai yi tsanani sosai ba. Saboda haka zazzabin ya fi tsanani jikin yara kanana." Idan aka yi magani da wuri, wanda ya kamu da maleriya zai murmuje, amma idan ta yi tsanani da wahala magunguna su yi wani tasiri. Haka zalika akwai kuma matsala ta bijirewa magunguna. Domin kwayoyin maleriya na da tarihin bijirewa magunguna, sabpoda haka allurar riga-kafi mai inganci sosai ke da matukar muhimmanci a cewar masana.