1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta amince da bai wa Ukraine tallafin yaki

April 21, 2024

Majalisar wakilai ta Amirka ta amince ta da tallafin dala biliyan 61 ga Ukraine domin ci gaba da yakar Rasha.

https://p.dw.com/p/4f17I
Majalisar Wakilai ta Amirka
Majalisar Wakilai ta AmirkaHoto: Jon Cherry/REUTERS

Majalisar wakilai ta Amirka ta bayar da tallafin dala biliyan 95 ga kasashen ketare a kuri'ar da aka kada wanda ba a saba ganin irinsa ba na samu goyon bayan bangarori biyu.

Babban kunshi tallafin shi ne na dala biliyan 61 da za a bai wa Ukraine wanda ya hada da makamai da za ta ci gaba da yakar Rasha. Isra'ila za ta samu kason dala biliyan 13 yayin da aka ware dala biliyan 9 a matsayin tallafi ga Zirin Gaza.

A yanzu za a mika bukatar kunshin tallafin da aka dauki watanni ana kai ruwa rana zuwa gaban majalisar dattawa domin ta aminci kafin ya isa gaban Shugaban kasar Joe Biden, wanda tun a shekarar da ta gabata yake kira ga 'yan majalisar da su mika bukatar.