1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta yi wa Ukraine tanadin makamai

September 8, 2022

Amirka ta shaida wa ministocin tsaron kasashe sama da 50 da ke taro a Jamus cewa za ta ci gaba da tallafa wa Ukraine kare kanta daga mamayar Rasha, inda ta sanar da tallafin sabbin makamai ga Ukraine.

https://p.dw.com/p/4GaIl
Deutschland | Lloyd Austin in der US Airbase Ramstein
Hoto: Andre Pain/AFP

Sakataren harkokin tsaron Amirka Lloyd Austin ya sanar da alkawarin kasarsa na bai wa kasar Ukraine karin tallafin da zai ba ta damar kare kanta da ya kai darajar Euro miliyan 658. Austin ya fadi haka ne a taron ministocin tsaron kasashe sama da 50 da ke adawa da mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine. Da safiyar Alhamis din nan ne dai aka bude taron a sansanin sojin sama na Ramstein da ke nan Jamus.

''Yakin na Ukraine ya dauki wani sabon salo. Dakarun Rasha na ci gaba da zaluntar birane da fararen hula a Ukraine ta hanyar jefa musu makamai masu linzami. To amma gwarazon sojin Ukraine na mayar da martani mai zafi wajen kare martabar kasarsu.'' in ji Austin

Austin dai ya shaida wa ministocin tsaron da ke halartar taron cewa, Amirka za ta horas da sojojin Ukraine domin ganin Kyiv ta samu damar ceton kanta daga hare-haren da fadar mulkin Rasha ta Kremlin ke kitsawa.