1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aljeriya ta nuna damuwa kan soke yarjejeniyar sulhu a Mali

Zainab Mohammed Abubakar
January 26, 2024

Aljeriya ta nuna matukar damuwa bayan da mahukuntan Mali da ke makwabtaka suka yi watsi da yarjejeniyar zaman lafiya, da ta shiga tsakani wajen cimma da 'yan tawayen a shekara ta 2015.

https://p.dw.com/p/4bjaw
Hoto: SOULEYMANE AG ANARA/AFP/Getty Images

Tun a shekara ta 2012 ne dai ake gwabza fada tsakanin  mayakan tawaye da na 'yan awaren kasar Mali, kuma Aljeriya ce babbar mai shiga tsakani a yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnati, da galibin kungiyoyin Abzinawa masu dauke da makamai suka rattabawa hannu a birnin Algiers.

Sai dai a jiya alhamis ne  mahukuntan mulkin sojan kasar ta Sahel, suka ayyana kawo karshen yarjejeniyar da ake ganin tana da matukar muhimmanci ga tabbatar da zaman lafiya a Mali, bayan shafe watanni ana gwabza fada.

Hakan na zuwa ne a yayin da dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD ke janyewa daga arewacin kasar mai fama da rikici.

Gwamnati a Bamako ta zargi "canji halin wasu kungiyoyin" da kuma zargin Aljeriyar da karbar bakuncin wasu wakilan kungiyoyin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar da a yanzu suka zama manyan 'yan ta'adda".