1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aljeriya ta dakatar da ayyukan raya kasa a Nijar

Gazali Abdou Tasawa MAB
January 4, 2024

Aljeriya ta fitar da Nijar da takwarorinta na kawancen AES Mali da Burkina Faso daga jerin kasashen da ke cin moriyar shirinta na raya kasashen Afirka, bisa zargin su da kusanci da Maroko da suke zaman doya da manja.

https://p.dw.com/p/4arle
Hukumomin Nijar da Aljeriya sun kwan biyu da fara aiki tare
Hukumomin Nijar da Aljeriya sun kwan biyu da fara aiki tareHoto: Präsidentschaft von Niger

Shirin raya kasashen Afirka na kasar Aljeriya wanda ke gudana a karkashin wata gidauniya mai kunshe da biliyoyin kudade ya tanadi bayar da bashi ga kasashen Afirka, ko tallafa masu ta hanyar aiwatar da ayyukan raya kasa da zuba jari a cikinsu. Sai dai a yanzu gwamnatin Aljeriya ta dauki matakin cire kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso da Guinea Conakry da Moritaniya daga jerin kasashen da za su ci moriyar shirin nata.

Karin bayani:Nijar ta bude kofofin cinikayya da arewacin Afirka

 Assimi Goïta na Mali da Abdourahamane Tiani na Nijar da Ibrahim Traoré na Burkina Faso
Assimi Goïta na Mali da Abdourahamane Tiani na Nijar da Ibrahim Traoré na Burkina FasoHoto: Francis Kokoroko/REUTERS; ORTN - Télé Sahel/AFP/Getty; Mikhail Metzel/TASS/picture alliance

Aljeriya na zargin kasahen musamman na sabon kawancen AES da ya hada Nijar da Mali da Burkina Faso da ke neman karfafa huldar kasuwanci da ta diflomasiyya da kasar Maroko, wacce ke zama babbar abokiyar gabarta a kan goyon bayan da take bai wa masu neman ‚'ancin gashin kai na yankin Polisariyo. Bana Ibrahim, fitaccen dan fafutika da ke goyon bayan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar, ya ce wannan ba abin damuwa ba ne kuma akwai hanyar da Nijar za ta mayar wa da kura aniyarta.

Karin bayaniMaroko za ta karfafa kasuwanci da kasashen Sahel uku

Wasu 'yan Nijar sun danganta matakin Aljeriyar da takun sakar da ta shiga da kasar Mali da  tasirin da mahukuntan Mali ke yi kan sabbin mahukuntan Nijar., a cewar Siraji Issa na kungiyar farar hula ta Mojen. Shi kuwa Boubacar kado da ke zama masanin tattalin arziki kana mai sharhi kan harkokin siyasa da diflomasiyya a Nijar cewa ya yi akwai mwata fargabar ta daban a cikin lamarin.

Karin bayani: Aljeriya: Warware rikicin Nijar ta diflomasiyya

Aljeriya ta taba sa hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da Nijar da Najeriya kan bututun gas
Aljeriya ta taba sa hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da Nijar da Najeriya kan bututun gasHoto: Chahine Sebiaa /IMAGO

Kawo yanzu, gwamnatin mulkin sojan Nijar ba ta ce uffan kan wannan matakin na kasar Aljeriya ba, wanda ya zo a daidai lokacin da kasar ke neman karfafa huldar kasuwanci da ita don iya amfani da tashar ruwan Algers wajen shigo da kaya ko kuma fita da su zuwa ketare.