1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al Gore ya yi kakkausar suka kan masu masaukin bakin COP28

December 3, 2023

Tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka kuma guda daga cikin masu rajin kare muhalli, Al Gore ya yi kakkausar suka kan Hadaddiyar Daular Larabawa, kasar da ke karbar bakuncin taron sauyin yanayi na duniya COP28.

https://p.dw.com/p/4ZjGy
Tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka Al Gore
Hoto: Kamran Jebreili/AP

Tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka kuma guda daga cikin masu rajin kare muhalli, Al Gore ya yi kakkausar suka kan Hadaddiyar Daular Larabawa, kasar da ke karbar bakuncin taron sauyin yanayi na duniya COP28.

A hirarsa da kamfanin dillancin labarai na Reuters, a wani bangare na tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan jigon taron, Al Gore ya ce mutumin da ke jagorantar taron Sultan Al-Jabeer, shi ne shugaban kamfanin man fetur da iskar gas na UAE, kuma yana sahun gaba na masu karya duk wata yarjejeniya da aka yi kan sauyin yanayi da ke da nasaba da gurbata muhalli.

Ya ce abin Allah wadai ne a ce kasar ta Hadaddiyar Daular Larabawa ta rasa wanda za ta nada ya jagoranci taron sai Al-Jabeer, yana mai nuna hakan da abin takaici matuka.

A kididdigar da ya gabatar a yayin taron, ya ce a bara Dubai ta fitar da iskar gas mai gurbata muhalli da kaso 7.5% wato kashi 1.5% na abin da kasashen duniya ke fitarwa, kamar yadda fasahar Artificial Intelligence da kuma wasu gamayyar kwararru suka tabbatar a wani binciken da suka gudanar.