1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaLibiya

Adadin wadanda suka mutu a Libiya ya karu

September 17, 2023

Sabbin alkaluman da ke fitowa daga Libiya, na nuna yadda ake samu karin gawarwaki daga barnar da ambaliya ta yi. A makon jiya ne ambaliyar ta yi ta'adi a yankin Derna na kasar.

https://p.dw.com/p/4WRrY
Bayan ta'adin ambaliya a yankin Derna
Hoto: Ayman Al-Sahili/REUTERS

Alkaluman da aka tantance na wadanda ambaliya ta yi sanadin su a Libiya sun kai akalla mutum dubu 11 da 300 a yanzu, a cewar ofishin kula da bayar da agaji na Majalisar Dinkin Duniya.

Ta'adin ambaliyar da ta auku a ranar Lahadin makon jiya, ya fi muni ne a yankin Derna da ke a gabashin Libiyar.

Bayanan da ke fitowa daga Beghazi a yanzu na cewa akwai yiwuwar samun karin wasu da za a iya rasawa, baya ga mutum 170 din da aka ce sun bata.

Wata mahaukayiar guguwa hade da ruwan sama mai lakabin Daniel, da ta shafi kasashe irin su Bulgaria da Girka da ma Turkiyya a baya-bayan nan ce dai ta afka wa Libiyar, inda ta daidaita birnin na Derna mai mazauna akalla mutum dubu 100.