1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

A Alhamis din nan ne kotun ICC za ta yanke hukunci kan Syria

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
November 16, 2023

Faransa ce ta ayyana izinin kamo Shugaba Bashar al-Assad bisa zargin tauye hakkin 'dan Adam

https://p.dw.com/p/4YrNI
Hoto: SANA/dpa/picture alliance

A Alhamis din nan ne kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta duniya da ke birnin Hague wato ICC, za ta yanke hukunci kan zargin take hakkin bil Adama da ake yi wa kasar Syria, sakamakon yadda bincikenta ya gano cewa an kashe dubban fararen hula tun bayan fara yakin kasar a shekarar 2011.

Karin bayani:Assad a taron kungiyar kasashen Larabawa

Kasashen Canada da Holland ne dai suka bukaci kotun ta gaggauta daukar matakin kawo karshen muzguna wa 'yan adawar kasar a kurkuku da gwamnatin Bashar al-Assad ke yi.

Karin bayani:'Yan Siriya na zanga-zangar kin al-Assad

Wannan na zuwa ne kwana guda bayan da Faransa ta ayyana izinin kamo Shugaba Bashar al-Assad, bisa zargin tauye hakkin 'dan Adam ta hanyar amfani da guba a shekarar 2013.