1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Siriya na zanga-zangar kin al-Assad

Binta Aliyu Zurmi MAB
April 23, 2023

Daruruwan al'ummar kasar Siriya sun gudanar da zanga-zanga don yin Allah wadai da yadda kasashen Larabawa ke kulla wata sabuwar dangantaka da gwamnatin Bashar al-Assad.

https://p.dw.com/p/4QSsa
'Yan Siriya sun saba gudanar da zanga-zangar kin jinin Bashar al-Assad
'Yan Siriya sun saba gudanar da zanga-zangar kin jinin Bashar al-AssadHoto: Ghaith Alsayed/AP/picture alliance

Boren da ya gudana a birnin Idlib na zuwa ne mako guda bayan da ministan harkokin kasashen ketare na Saudiyya ya gana shugaba Bashar  al-Assad na Siriyaa birnin Damascus, Wannan ziyara na zama irinta ta farko a shekaru 12 bayan da yaki ya barke a kasar.

Kazalika jami'an diflomasiyyar kasashen Saudiyya da Tunisiya da Masar sun yi wata ganawa da ke da zummar lalubo hanyoyin kawo karshen yakin da ya daidaita kasar. Siriyawan dai na neman kasashen duniya musamman na yankin Gabas ta Tsakiya da su ci gaba da mayar da shugabansu saniyar ware, saboda ba son kowace kasa ta saka musu baki don ba za su taba daidaitawa da al- Assad ba.