1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jaridun Jamus kan nahiyar Afirka

Mouhamadou Awal Balarabe AMA(SB)
May 27, 2022

A sharhunansu, jaridun Jamus sun mayar da hankali kan ziyarar da shugaban gwamnati Olaf Scholz ya kai wasu kasashen Afirka da suka hada da Senegal da Afirka ta Kudu da Nijar.

https://p.dw.com/p/4Bwqq
Niamey, Niger | Kanzler Scholz besucht den Niger
Niamey, Niger | Shugaba Bazoum da Olaf ScholzHoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Frankfurter Allgemeine Zeitung ta wallafa sharhi ne mai taken Neman hadin kan Nijar a kan matsalar tsaro a yankin Sahel, inda ta ce ba kasafai ake samun manyan baki da yawa a cikin dan gajeren lokaci a Jamhuriyar Nijar ba. Amma daga tsakiyar watan Afrilu kawo wannan lokaci, ministar harkokin waje Jamus Annalena Baerbock da Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da kuma shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz sun ziyarci kasar ta Nijar.  Wannan kasa ta zame wa sojojin kasashen yamma wata sabuwar cibiya ta yaki da 'yan ta'adda, bayan da Faransa ta janye sojojinta daga Mali tare da jibge su a Nijar.

Jaridar ta ci gaba da cewa shugaban kasa Mohamed Bazoum da gwamnatinsa ta ba wa Faransa hadin kai a yaki da ta'addanci, amma kuma wannan mataki na tattare da hadari. Wannan kasa mai mutane miliyan 24, wacce kuma ta ninka Jamus sau uku da rabi a fadi, ta kasance wageggiyar kofa  ga masu kaifin kishin Islama. Suna amfani da talauci da rashin gamsuwar al'umma dangane da kamun ludayin gwamnti da rikice-rikice don yaduwa zuwa sauran kasashe na yammacin Afirka. 

Afirka ta Kudu ta nuna wa Scholz adawaJaridar Süddeutschezeitung ta bayyana cewa Afirka ta Kudu ta yi adawa da takunkumin da aka kakaba wa Rasha. Jaridar ta ce Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu bai furta kalmar yaki ko sau daya ba, lokacin da ya yi arba da shugaban gwamnatin Jamus Olaf scholz, duk da  kokari da bakonsa ya yi wajen nuna masa cewa Rasha ta zalunci Ukraine sakamakon mamaye ta da ta yi. Sai dai Ramaphosa ya bayyana cewa ta hanyar tattaunawa ne kawai za a kawo karshen abin da ya danganta da "rikici".

Ziyarar Olaf Scholz a Afirka ta Kudu
Ziyarar Olaf Scholz a Afirka ta Kudu Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

 

Karancin abinci na addabar nahiyar Afirka 

Jaridar Neues Deutschland ta wallafa sharhi mai take: yake-yake nai haifar da 'yunwa, inda ta ce yankunan Afirka da bala'i ya rutsa da su na fama da haihuwar farashin masarufi da karancin na sa wa a bakin salati. Ta kara da cewa tashin gworon zabi da man fetur ya yi ba wai barazana kawai yake ga yanayin abinci na miliyoyin mutane ba, amma yana kara ta'azzara matsalar 'yunwa a Afirka. 

Rahoton ya ambato tsokacin Shirin samar da Abinci na Duniya wanda ya ce yana bukatar karin miliyan  951 ba dallar Amirka cikin gaggawa don tinkarar ja'ibar 'yunwa a Afirka, bayan da ta kunno a yammacin Afirka da Arewa maso yammacin nahiyar. A kasashe da yawa, fari da karancin amfanin gona sun haifar da karancin abinci, baya ga karuwar tashe-tashen hankula wadanda ke karan tsaye ga noma da safarar abinci. 

Za a gina masana'antar batir ta farko a KwangoJaridar Handelsblatt ta ce wata kasa ta Afirka ta samu ci gaba a fagen bada gudunmawa wajen kera motoci, wacce ba wata ba ce illa Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango. DRC ce kasa mafi girma a duniya da ke samar da cobalt, karfen da masana'antu ke amfani da su wajen kera batura motoci. Hasali ma a duniya baki daya tana da kashi biyu bisa uku na yawan wannan ma'adini, kuma ba ta da niyar tsayawa a matakin samar da albarkatun karkashin kasar kawai. Amma gwamnatin Kinshasa na son sarrafa cobalt din a cikin gida don ta fi amfana. 

Kamfanin hada batura na Jamus Bosch
Kamfanin hada batura na Jamus BoschHoto: Bosch

An tsara gina masana'antar samar da batir a Kwango wacce za ta fara aiki a karshen shekarar 2023. DRC ta kulla yarjejeniyar hadin gwiwa da makwabciyarta Zambiya, wacce ita ma ke da arzikin ma'adanai domin samar da baturan motoci. Wannan zai bai wa kasar damar rubanya hulda da manyan kamfanonin Turai ciki har da Bosch, da wasu kamfanoni na kasar Sin ko Chaina.