1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Goyon bayan mazauna Zirin Gaza

Mahmud Yaya Azare SB/ATB
October 13, 2023

Dubun-dubatar mutane a kasashen Larabawa sun yi zanga-zangar nuna goyon baya ga mazauna yankin Zirin Gaza na Falasdinu da Isra'ila ke ci gaba da killacewa.

https://p.dw.com/p/4XWLH
Indonesiya | Goyon bayan mutanen zirin Gaza
Indonesiya ana goyon bayan mutanen zirin GazaHoto: Devi Rahman/AFP/Getty Images

Dubban mutane a garin Ramallah da ke yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan sun rera taken nuna goyon baya ga mazauna yankin Zirin Gaza. A kasar Siriya ma, inda jiragen yakin Isra'ila a kwanaki biyun da suka gabata, suka halaka sojojin kasar bakwai a wasu hare-haren da suka ce na kan-da-garki ne kan filayen jirgin birnin Demascus da Aleppo. Limamin Masallacin Bani Umayyah Muntasir Ja'afar ya yi kira ga shugabanin Larabawa da kar su bari a kori mazauna Zirin Gaza daga yankinsu.

Karin BayaniGaza zai iya ruruta rikicin Isra'ila da Hezbollah

A Masar kuwa, duk da aiki da dokar haramta zanga-zanga kusan tsawon shekaru takwas a kasar kungiyar 'yan jaridar kasar ta shirya wani gangami, inda suka soki yadda hare-haren da Isra'ila ke kai wa a yankin Zirin Gaza ke ritsawa  da 'yan jaridun da ma masu ayyukan agaji a farmakin da take kai wa yankin zirin Gaza. Shi kuwa limanin haramin Makka da ya jagoranci sallar Juma'a, addu'a ya yi cikin koke-koke, ga wadanda suka kwanta dama sakamakon rikici.