1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaZimbabwe

ZANU-PF ta lashe mazabu 43 a Zimbabuwe

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 25, 2023

Sakamakon farko na kuri'un da aka kidaya bayan kammala zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki a Zimbabuwe, na nuni da cewa jam'iyya mai mulki ta ZANU-PF da kuma babbar jam'iyyar adawa CCC na kan-kan-kan.

https://p.dw.com/p/4VaPz
Zimbabuwe | Zabe | Shugaban Kasa
Fara kirga kuri'un da aka kada a babban zaben ZimbabuweHoto: Mkhululi Thobela/Anadolu Agency/picture alliance

Jam'iyyar Shugaba Emmerson Mnangagwa ta ZANU-PF mai mulki a Zimbabuwen dai, na fatan ci gaba da rike  kaso 43 cikin 100 da ta samu a kasar. Ya zuwa yanzu sakamakon da Hukumar Zabe ta Zimbabuwen ta fitar, na nuni da cewa jam'iyyar ta ZNU-PF ta lashe mazabun 'yan majalisun Tarayyar 43 yayin da jam'iyyar adawa ta CCC ke da 37 cikin 210 din da ake da su a kasar. Ba a dai fara bayyana sakamakon zaben shugaban kasa ba wanda Shugaba Emmerson Mnangagwa mai shekaru 80 a duniya ke neman tazarce, a daidai lokacin da al'ummar kasar ke fama da matsanancin talauci.