1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman tattauna batun fitar da hatsi daga Ukraine

Binta Aliyu Zurmi
July 13, 2022

An fara zaman tattaunawa tsakanin Rasha da Ukraine a kan takadamar fitar da hatsi daga tashoshin ruwan kasar Ukraine da ake zargin Rasha da dakatar wa.

https://p.dw.com/p/4E4YX
Symbolbild Ukraine Getreide
Hoto: Dado Ruvic/REUTERS

Wakilan kasashen Rasha da Ukraine da ke gwabza fada da juna sun fara tattaunawa a kan batun jigilar hatsi zuwa ketare a birnin Santanbul na Turkiyya.

Zaman tattaunawa da ake yi karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya da na mahukuntan Ankara na zuwa ne bayan da ake ci gaba da zargin Rasha da hana fitar da tarin alkama da ke jibge a tashoshin ruwan Ukraine tun bayan da ta mamaye kasar.

Wannan dai shi ne zama na farko da wakilan kasashen Rasha da Ukraine ke yi karkashin inuwa daya tun bayan wanda suka yi na keke da keke a kokarin kawo karshen rikicin da ke tsakaninsu a watan Maris din da ya gabata.

Ana fatan samun maslaha a wannan zama da zai kawo karshen karancin hatsi da duniya ke fuskanta sakamakon rikicin da kasashen biyu ke yi.