1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Zaben shugaban kasa zagaye na biyu

Abdul-raheem Hassan
February 21, 2021

Miliyoyin al'umma za su tantance sabon shugan kasa tsakanin 'yan takara biyu Mazoum Mohammmed dan takarar jam'iyyar PNDS da Mahamane Ousmane na jam'iyyar RDR Canji.

https://p.dw.com/p/3peVW
Niger Niamey | Wahlen
Hoto: Issouf SANOGO/AFP

Dan takarar jam'iyya mai mulki Mohammmed Bazoum ya samu kashi 39.3 na kuri'un zagaye na farkon zaben, shi kuwa Mahamane Ousmane ya tsira da kashi 16.9 na kuri'u a zagayen farko na zaben.

'Yan takarar da suka zo na uku da na hudu a zagayen farko na zaben shugaban kasar na marawa Bazoum baya a zaben yau, inda gamayyar jam'iyyun hamayya 18 ke sa ran marawa shi kuma Ousmane yana sa ran samun goyon baya daga gamayyar jam'iyyun hamayya 18 ke sa ran marawa Ousmane baya.

Akalla mutane miliyan 7 da dubu 400 ne ke da damar kada kuri'unsu a zaben na yau cikin adadin al'ummar Nijar miliyan 22, rahotanni na cewa an girke dubban sojoji a fadin kasar saboda tsaro, batun tsaron na cikin manyan matsalolin da ke jiran wanda zai yi nasara a zaben.

Nijar dai ta fuskanci sauyin gwamnati da tsinin bindiga har sau hudu, sai dai wannan shi ne karon farko da kasar za ta mika mulki cikin ruwan sanyi tsakanin shugabannin fararen hula tun bayan samun 'yancin kai daga Faransa a 1960.