1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Zaben Masar ya dauki hankalin Jaridun Jamus

Zainab Mohammed Abubakar
December 16, 2023

A zaben Masar, nasarar Al-Sisi ta tabbata kasancewar ba shi da abokin hamayya na hakika

https://p.dw.com/p/4aFNo
Ägypten Kairo 2023 | Präsidentschaftswahl | Präsident Abdel Fattah al-Sisi bei Stimmabgabe
Hoto: Egyptian Presidency Media Office via AP/picture alliance

A Masar, nasarar Al-Sis a zaben shugaban kasai ta tabbata kasancewar ba shi da abokin hamayya na hakika", wannan shi ne taken labarin da jaridar Die Tageszeitung ta  wallafa a kan sakamakon zaben. Jaridar ta ce, ko matsalar tattalin arziki ba ta jefa shi cikin bazaranar samun nasara a zaben ba. Tuni aka ayyana Abdel Fattah al-Sisi, wanda ke kan karagar mulki a matsayin wanda ya lashe zaben. A halin yanzu dai kasar na fama da matsalar tattalin arziki mai tsanani. Yanayi na mulkin kama-karya na soja yana danne abokan hamayya, inda ake tsare su tare da azabtar da su.

Zaben shugaban kasa a Masar
Hoto: Mohamed Elshahed/Anadolu/picture alliance

'Yan takarar shugaban kasa uku da ke adawa kusan na jeka na yi ka ne, wadanda suka hada da Hasem Omar na jam'iyyar Republican People's Party wanda ya kasance hamshakin attajiri ne kuma mai goyon bayan al-Sisi, da kuma Farid Sahran na jam'iyyar Social Democratic Party da ake wa kallon yana da kusanci da shugaban kasar da kuma jami'an tsaro. Ya taimaka wajen kafa majalisar ministocin al-Sisi bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a shekarar 2013.

Sai kuma Abdel-Sanad Ja-mama daga jam'iyyar Wafd wanda ya ce ya na son "ceto Masar", amma ba ya sukar manufofin gwamnati. Fitaccen dan adawar siyasa daya tilo shi ne tsohon dan majalisa Ahmed al-Tantawi, wanda aka tilasta wa janye takararsa a watana Oktoba.

Magoya bayan shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi
Hoto: Amr Nabil/AP Photo/picture alliance

Ita kuwa jaridar Zeit Online sharhi ta yi game da kammala janye rundunar Jamus daga Mali. Jaridar ta ce, ragowar sojojin Jamus na Bundeswehr a karkashin rundunar kiyaye zaman lafiya ta MINUSMA a Mali, sun bar sansaninsu na karshe a Gao. A cikin shekaru goma na aikin zaman lafiya da Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar, Jamus ta tura jami'anta na soji kusan 20,000

Jamus ta kawo karshen aikinta a karkashin Majalisar Dinkin Duniya a kasar Mali da ke yammacin Afirka bayan fiye da shekaru goma. Sojojin Jamus 142 na karshe a tawagar wanzar da zaman lafiya ta MINUSMA sun bar sansaninsu da ke Camp Castor da ke wajen filin jirgin saman Gao, kamar yadda rundunar sojojin Jamus ta sanar.

Jamus  din dai ta dauki watannin wajen kwashe jami'an sojin na ta daga Mali, lamarin da ya kara yin wuya bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar da ke hada iyaka da Mali, da yadda dangantarsu ta zama mai sarkakiya duk da cewa suna dasawa a baya.

Sojojin Jamus a lokacin da suke janyewa daga kasar Mali
Hoto: Ronny Hartmann/AFP

Jaridar Handelsblatt ta wallafa sharhinta a kan sakamakon taron sauyin yanayi na COP28 da aka gudanar a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa.  Jaridar ta ce Afirka ta zargi kasashen yamma da mulkin mallakar tattalin arziki.

Idan yawan al'ummar Afirka suka karu a cikin shekaru masu zuwa, za a iya fuskantar karuwar hayaki mai guba na carbon dioxide a nahiyar. Kasashen yammacin duniya na fargabar hakan, a kan´haka ne suke kira ga kasashen Afirka da su yi watsi da amfani da kwal da iskar gas da kuma mai cikin gaggawa, batun da ya haifar da takaddama a taron na COP28.

Ministan makamashi na Ghana, Matthew Opoku Prempeh, alal misali, ya fusata inda ya dasa ayar tamba, "shin kasashen yamma suna son mu ci gaba da kasancewa marasa ci gaba ne?". Sauran wakilan kasashen Afirka sun yi gargadi da nuna cewa takwarorinsu na yamma da ke da arzikin masana'antu suka haddasa matsalar yanayin da duniya ke fuskanta a yanzu.