1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargaba kan yunkurin kwace birnin Bakhmut

Ramatu Garba Baba
December 3, 2022

Manyan kasashen duniya sun soma baiyana fargaba kan abin da zai biyo bayan yunkurin rundunar Rasha na son ganin ta kwace iko da birnin Bakhmut da ke Ukraine

https://p.dw.com/p/4KQuJ
Ukraine-Krieg | Armee kämpft mit Schlamm an der Front
Hoto: Metin Aktas/AA/picture alliance

Kasashen yamma na baiyana fargaba kan wani sabon yunkurin Rasha na kwace ikon birnin Bakhmut da ke Ukraine, an gano yadda rundunar Rashan ke kokarin ganin ta yi wa birnin kawanya, masana sun ce sun hango barazanar da wannan nasara ka iya jefa wasu yankunan da ke kawayen birnin na Donetsk.

Britaniyya na daga cikin kasashen da ke baiyana damuwa a game da wannan sabon salon yakin da Rasha ta dauko da tuni ya soma shan suka daga kasashen da ke goyon bayan Ukraine a fadan da suke da Mosko. 

Shugaba Volodymr Zelensky a na shi bangaren kuwa, kira ya yi, na a rage farashin man Rasha a kasuwannin duniya, yana mai cewa, hakan zai yi matukar tasiri a karya tattalin arzikin kasar da ke mamayar Ukraine.

Rasha dai ita ce kasa ta uku a duniya wajen samar da mai bayan Amirka da Saudiyya, kuma kusan rabin man da ta ke fitarwa na zuwa kasashen Turai.