1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan IPOB na kuntata wa jam'a a Ebonyi da Abia

Muhammad Bello MAB
July 5, 2023

'Yan rajin Biafra na kungiyar IPOB sun umarci jama'a da su ci gaba da zaman dirshan a gidajensu na tsawon kwanaki bakwai. Sai dai wasu mutanen na yin watsi da matakin, lamarin da ke haddasa salwantar rayuka da dukiyoyi.

https://p.dw.com/p/4TRq3
'Yan rajin Biafra sun juma da fara zanga-zanga a NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/P. U. Ekpei

 

Wani bangare na kungiyar IPOB na ci gaba da sintiri da muggan makamai a sassan yankin Kudu maso babashin Najeriya don tilasta wa jama'a bin umarnin zaman gida na kwanaki bakwai. Wannan gararin ya fi tsananta a jihar Ebonyi, inda jama'a da dama suka kaurace wa kasuwanni da makarantu da ofisoshin gwamnati da ma kamfanoni masu zaman kansu da bankuna du suka kasance a rrufe.

'Yan IPOB da ke rufe fuskokinsu sun fara bindige mutane da suka gani a kan tituna, musamman a wasu sassan Abakaliki babban birnin jihar Ebonyi. Sun kuma bude wuta kan wata kasuwa da mutane ke tsaka da ci tare da far ma jami'an 'yan sanda da kona motocinsu. jagoran masu sintirin na cewar: " A nan kasuwar Abakaliki, ku kona komai, kar ku bar komai, zaman gida dole ne, idan ba a sako Nnamdi Kanu ba to ba zaman lafiya."

Hukumomin jihar Ebonyi sun jaddada cewar suna iya kokarinsu don dawo da doka da oda, tare da yin kiraye-kiraye ga jama'a da su kwantar da hankula, gami da fitowa don ci gaba da harkoinsu na yau da kullum.

Jihar Anambra ta ki bada kai ga IPOB

Nigeria Onitsha brennende Reifen Biafra Konflikt
'Yan IPOB sun yi kone-kone a jihar EbonyiHoto: Getty Images/AFP/P.U. Ekpei

A jihar Anambra kuwa, shugabannin siyasa irin su  Sanata Ifeanyi Ubah na kai gwauro da mari a sassan jihar, tare da hada gangamin jama'a don a bijire wa umarnin na IPOB. Sanata Ifeanyi Ubah da ya jagoranci wata zanga zanga ya ce: " Ni da jama'armu ba za mu yarda da ci gaba da zaman gida ba, za mu ringa fita duk ranar litinin."

Tun kwanakin baya ne jihar Enugu ta ayyana sa kafar wando daya da m su bin umarnin na IPOB. Amma an samu karancin kai kawon jama'a duk da girka jami'an tsaro da aka yi a sassa da dama. Gwamnatin jihar ta yi barazanar janye lasisin gudanarwa na makarantun da suka rufe karantarwar kan hujjar bin umarnin na IPOB. A Jihohin Imo da Abia ma dai a na zaman dar-dar. Ko da Malam Bashir, mazaunin Aba ne jihar Abia, sai da ya ce daya daga cikin shugabannin IPOB ya shigo jihar amma jami'an tsaro sun fatattake shi.

IPOB: An sami Nnamdi Kanu ko mu ci gaba

Nigeria Biafra | Nnamdi Kanu
'Yan IPOB na nema a saki Nnamdi Kanu Hoto: DW/K. Gänsler

Wani bangare na kungiyar ta IPOB da Mr Emma Powerful ke magana da yawunta na nuna rashin hannun IPOB a wannan umarni. Sai dai Simon Ekpa dan kungiyar na IPOB mazaunin kasar FinLand na bugan kirjin assasa umarnin na zaman gida, inda ya ce manufar iitace matsa lamba ga gwamnatin Najeriya na ta sako jagoransu Nnamdi Kanu da ke tsare bisa tuhumarsa da laifuka da dama da suka hada da cin amanar kasa da kuma tunzura jama'a ga yi wa gwamnati bore.