1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sonko

Zainab Mohammed Abubakar
July 14, 2023

Babbar jam'iyyar adawa ta Senegal a ayyana shugabanta Ousmane Sonko a matsayin dan takararta, a zaben shugaban kasa tare da watsi da tambayoyi game da cancantar sa.

https://p.dw.com/p/4Tw3a
Senegal | Ousmane Sonko
Hoto: Seyllou/AFP/Getty Images

A jiya Alhamis ne aka zabi Sonko a matsayin dan takarar jam'iyyar PASTEF-Patriots na zaben shugaban kasa da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairun 2024, in ji jam'iyyar a cikin wata sanarwa ga kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.

Wakilai sun kada kuri'a a sassa 46 na kasar ta Senegal da kuma 'ya'yanta da ke zama a wasu kasashen waje, kuma babbar hukumar gudanarwar jam'iyyar ce ta tabbatar da sakamakon.

Ousmane Sonko ya samu karbuwa a tsakanin matasan Senegal da ke fama da rashin gamsuwa da gwamnati mai ci, ta hanyar yin kamfe mai zafi  a kan shugaba Macky Sall, na nuna shi a matsayin mai cin hanci da rashawa kuma mai mulkin kama-karya.