1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki da kwararowar hamada a Nijer

December 22, 2011

A birnin Tahoua na jamahuriyar Nijar, ana gudanar da wani babban zaman taro dake duba hanyoyi rage matsalolin da canjin yanayi kan iya haifarwa, a fannoni kamar na noma da kiwo.

https://p.dw.com/p/13XwR
Wüste im Niger, undatierte Aufnahme. Quelle: dpa
Karancin ruwan sama a Nijar

A birnin Tahoua na jamahuriyar Nijar, ana gudanar da wani babban zaman taro dake duba hanyoyi rage matsalolin da canjin yanayi kan iya haifarwa, a fannoni kamar na noma da kiwo.

Wannan zaman taro da kungiyar CNEDD mai kula da canjin yanayi , dake kalkashin ofishin Praminista na jamahuriyar Nijar ta shirya, na bayar da horo ga Spetoci na makarantu, tare da zababbu na kananan hukumomi da aka gayyato daga kananan hukumomi guda guda da aka zaba daga ko wata jiha ta kasar nan, wanda suka fi fuskantar matsalolin canjin yanayi , inda daga nasu bangare zasu yada fusa'o'in da suka koya wajan wannan zaman taro kan canjin yanayi, da zimmar bin hanyoyin da suka fi sauki da zasu bada damar samun sassauci ga matsalolin da canjin yanayi kan iya haifarwa. Malam Abdullaye Issa, jami'i ne dake wannan kungiya mai kula canjin yanayi ta kasa, ya mana karin haske, yana mai cewa:

"Kunsan malumai sune masu bayar da labarai a cikin karkara sabili da haka muke ganin idan muka basu horo, to su zasu sanar da saran malumai, sannan su kuma su sanar da yara yan makanranta yayin dasu kuma zasu sanar da iyayan su matsalolin da canjin yanayi ke haddasawa da kuma matakkan dauka."

Babban burin dai a nan shine tun da Jamahuriyar Nijar ta sa hannu ga kundi na duniya na canjin yanayi, wannan zaman taro zai yi bitar ayukan da akayi a wannan fanni kamar na samar da irin shuka mai gawgawa na hatsi, dawa da wake da aka jarraba a cikin karkara ganin cewa a halin yazu rowan damina bassa jimawa, inda Malam Abdullaye Issa na kungiyar kula da canjin yanayi yake cewa:

"Yanzu ruwan sama, basu wuce kwana sittin, sittin da biyar zuwa saba'in, shi ya sa muka samu irin zamani muka sa musu. Ina ganin duk karamar hukumar da muke aiki dasu an zabi manoma arba'in arba'in mata da maza, wanda ake jarraba wannan fusa'a da su, kuma sunce sosai akwai dacewa, dan haka ana so nan gaba a san yadda za'a yada wannan fusa'a ga sauran kananan hukumomi kafin wannan tsari ya kawo karshen sa, saboda a samu ciyo kan matsalar."

Mahalarta taron sun yaba wannan haduwa inda suke ganin cewa kowa zai karu da kokarin da wata karamar hukuma keyi wajan rage ko magance radadin canjin yanayi Amadu Atche shine shugaban karamar hukumar mulki ta Kaou, wadda aka zaba a cikin Jihar Tahoua yana mai cewa:

A view looking down from the escarpment of the Falaise de Bandiagara that extends 150km through the Sahel of Dogon villages on the dry plains, Mali 30 April 2007. While environmental experts meet in Bangkok this week hammering out details of a report on ways to fight climate change life in Africa's Sahel becomes increasingly more difficult with desertification and temperature rise due to climate change making farming and the survival of livestock increasingly more desperate. EPA/NIC BOTHMA +++(c) dpa - Report+++
Kwararowar hamadaHoto: picture-alliance/ dpa

"Kamar wannan haduwa da mukayi, ko wace jiha akwai karamar hukuma daya da aka dauka da ake ganin tafi ko wacce matsala, kenan idan aka canza fusa'o'i tsakanin wa'innan kananan hukumomi, za'a samu babban ci gaba, kuma an kawo mana iri mai gawgawa,wanda komin karancin ruwa ana iya samun anfanin shi, kenan ta haka ana ganin canjin yanayi ba zai haifar da babbar matsala ba idan aka ci gabaa da haka."

Sau tari dai ana gudanar da tarurruka kan matsalar dumamar yanayi inda bayan na Copenhagen a bana kuma aka gudanar da wani a kasar Afrika ta kudu, inda wakillan kasashen Afrika dake halartar irin wadannan tarurruka na kira ne ga kasashe masu manyan masana'antu da su rage fitar da hayaki mai yawa kuma su bayar da tallafi ga kasashe masu tasowa ta yadda zasu fuskanci duk wata matsala da canjin yanayi kan iya kawa.

Mawallafi: Salissou Boukari

Edita: Umaru Aliyu