1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNa duniya

Wasanni: Masar ta mamaye gasar wasannin Afirka

Mouhamadou Awal Balarabe
March 25, 2024

Masar ta mamaye gasar wasannin Afirka da aka kammala a kasar Ghana yayin da Jamus ta mamaye Faransa a wasan sada zumunta gabannin gasar kwallon kafar Turai,

https://p.dw.com/p/4e6MF
Magoya bayan kungiyar kwanllon kafar Ghana
Hoto: Isaac Ortiz/Agencia MexSport/IMAGO

Masar ce zakaran da Allah ya nufa da cara a gasar wasanni daban-daban na kasashen Afirka da aka fi sani da all Africa games da Ghana ta dauki bakunci, inda ta samu jimillar lambobi 189 ciki har da Zinare 101. Ita kuwa Najeriya ta samu matsayi na biyu sakamakon lambobin 121 ciki har da zinare 47 da ta lashe yayin da Afirka ta Kudu ta zo a matsayi na uku da lambobi106 ciki har da zinare 32. A Nata bangaren, Ghana da ta tashi a matsayi na shida ta samu ci gaba idan aka kwantanta da gasar karshe a Maroko inda suka samu 17, alhali a  gida Accra sun samu lambobin 67 ciki har da zinare 19 da azurfa 29 da tagulla 19.

Kimanin 'yan wasa 5,000 ne suka fafata a fannoni 29 a garuruwa biyu na Ghana ciki har da babban birnin Accra. Hasali ma shugabannin wasanni da su 'yan wasa su kansu sun bayyana gamsuwarsu da yadda gasar karo 13 da Ghana ta gudanar ba tare da tare da matsala ba. Su ma ma'abota kwallon kafa da sauran wasanni sun halarci filayen wasa. Alal hakika ma dai, kungiyar 'yan kasa da shekaru 20 da haihuwa ta Ghana ce ta lashe kofin kwallon kafa na gasar wasannin Afirka bayan da ta samu nasara a kan takwararta ta Yuganda da ci 1-0.

Zakarun AFCON
Hoto: Themba Hadebe/AP/picture alliance/dpa

kungiyoyin kwallon kafa na kasashen Afirka sun koma fagen daga watanni biyu bayan kawo karshen gasar cin kofin kwallon wannan nahiya da ta gudana a Côte d' Ivoire. Hasali ma sun yi amfani da ranakun da FiFA ta ware a watan Maris domin gudanar da wasannin sada zumunci tsakanin kasa da kasa da nufin shirya wa sabuwar gasar duniya da ake wa lakabi da FiFA series da za a kaddamar cikin shekaru biyu masu zuwa. Sannan kuma a daya gefe, tawagogin na Afirka na sharar fage game da wasanni neman cancantar shigar gasar AFCON ko CAN da za ta gudana a Maroko a badi idan Allah ya kai mu.

Sai dai Côte d' Ivoire da ke rike da kofin kwallon kafa na Afirka ta sha kashi a hannun Benin, inda aka tashi 2-2. Ita kuwa Mali ta lallasa Moritaniya da ci 2-0 yayin da Togo ta jibgi Mena ta Nijar da 2-1. A nata bangaren Senegal ta mamaye Gabon da ci 3-0 yayin da Tunisiya ta sha kashi a bugun fenariti a hannun Croatia a gasar sada zumunta da aka yi a Masar. Aljeriya kuwa ta lallasa Boliviya da ci 2:0 yayin da Tunisiya ta tashi 0:0 da Croatia.

Karawar Jamus da Faransa
Hoto: Helge Prang/GES/picture alliance

A nahiyar Turai ma, kasashe da dama sun gwada kwanji a wasannin sada zumunci da nufin shirya gasar cin kofin nahiyar Turai da za ta gudana a Jamus. Kuma abin da ya fi daukar hankali shi ne nasarar da Jamus ta samu a kan Faransa da ci 2-0 a birnin Lyon, lamarin da ya dora Mannschaft kan kyakkyawar turba watanni kafin fara gasar Euro a gida. Abin sha'awar ma, shi ne kwallon da Florian Wirtz ya ci bayan dakika takwas da fara wasa, yayin da Kai Havertz ya zura kwallo na biyu bayan da aka dawo hutun rabin lokaci, lamarin da ya sanya babban kocin Jamus Julian Nagelsmann farin ciki:

"Ban sani ba ko za a kwatanta shi da kwanciyar hankali, amma na yi matukar farin ciki game da yadda kungiyata ta taka leda. Mun fuskanci karshen kakar wasan 2023 cikin sarkakiya, don haka ina matukar farin ciki da ‘yan wasana, domin nasara ce da za ta karfafa musu gwiwa. Ya kamata mu ci gaba da haka, wato gudanar da wasa cikin nishadi. Tawagar ta bi tsarin da na shirya sau da kafa, ni ma na yi farin ciki sosai."

Ita kuwa Ostirya ta doke Slovakiya da ci 2-0 yayin da Italiya ta doke Ecuador da ci 2-0. Iraland da Beljiyam sun tashin wasansu na sada da zumunci ba wanda ya ci wani, haka suma Danmark da Switzerland sun tashi 0-0, yayin da Ingila ta dibi kashinta a hannun Brazil da ci 0-1. A wani abun da ke zama mummunan labari ga kasar ta Ingila ma, mai ruwan kwallaye na Bayern Munich kuma kyaftin din Ingila Harry Kane ya ji rauni a idon sawun, lamarin da zai hana shi buga wasan sada zumunci da kasarsa za ta yi da Beljiyam  ranar Talata. Shi dai Kane ya kasance dan kwallon Ingila da ya fi zura kwallo a kasarsa, kuma a yanzu haka ya ci wa Bayern Munich kwallaye 31.

Har yanzu muna fagen kwallon kafa, amma a wannan karon a tarayyar Najeriya, inda aski ya fara zuwa gaban goshi a kokarin da kungiyoyin kwallon kafar kasar ke yi na lashe kambun zakara a kakar wasa ta 2023/2024. A yanzu haka ma dai, kungiyar Enugu Rangers daga kudancin kasar ce ke jan ragamar teburin gasar, a daidai lokacin da aka shiga mako na 27. Amma kasancewar an fuskanci jinkiri wajen daidaita al'amura daga hukumar kwallon kafa ta Najeria kafin fara gasar ta bana, ko kwalliya ta biya kudin sabulu?

Dan wasan Tennis Jannik Sinner a karawarsa da Daniil Medvedev
Hoto: Alessandra Tarantino/AP/picture alliance

A fagen tennis, dan Italiya Jannik Sinner da ke a matsayi na uku a duniya ya jijjigu a hannun Tallon Griekspoor mai matsayi na 26, kafin ya cancanci kai wa zagaye na gaba na Masters 1000 Miami, yayin da Holger Rune mai matsayi na bakwai ya fice daga gasar tun a zagaye na biyu bayan da Fabian Marozsan ya doke shi. Sai dai a bangarensa, dan kasar Spain Carlos Alcaraz da ke zama gwarzon tennis na duniya bai sha wata wahala wajen yin waje road da takwaransa Roberto Carballés da ci 6-2, 6-1 ba. Shi kuwa Danil Medvedev dan kasar Rasha mai matsayi na uku a duniya ya kawar da dan Birtaniya Cameron Norrie da jerin ci 7-5, 6-1, yayin da Bajamushe Alexander Zverev da ke biya masa baya a matsyi na hudu ya yi nasarar doke dan kasar Canada Félix Auger da jerin ci 6-2, 6-4.

 A bangaren mata kuwa, da gumin goshi ne Swiatek ta kawar da Noskova, lamarin da ke bata damar buga wasanta na gaba da Ekaterina Alexandrova ta kasar Rasha. Ita kuwa 'yar kasar Faransa Caroline Garcia mai shekaru 27 da haihuwa ta sake haduwa da Naomi Osaka mai shekaru 29 a karo na uku a bana. amma dai  Bafaranshiyar ta doke Osaka  da ci 7-6 (7/4), 7-5. Garcia za ta hadu a zagaye na gaba na gasar Miami na Amurka da Coco Gauff mai matsyi na uku a duniya, wacce ta doke 'yar Faransa Océane Dodin da jerin ci 6-4, 6-0.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani