1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wankin babban bargo ga zabukan Najeriya

June 27, 2023

Masu sanya idanu na Kungiyar Tarayyar Turai a lokacin babban zaben Najeriya suka ce dimukuradiyyar kasar na fuskantar koma baya sakamamkon gazawa ta masu ruwa da tsaki da tsari na zabukan kasar.

https://p.dw.com/p/4T8Df
Matasa sun bayar da gudun mawa a matakai daban daban na zabukan Najeriya
Matasa sun bayar da gudun mawa a matakai daban daban na zabukan NajeriyaHoto: Christopher Onah/Focal Point Agency/IMAGO

Masu sanya idanun na EU sun yi suka ga daukaicn tsarin zabukan tarrayar Najeriyar na shekarar 2023, kama daga yakin neman zabe ya zuwa ga halayyar 'yan siyasa ta kasar da ma uwa uba gazawa ta hukumar zabe mai zaman kanta INEC. Cikin rahoton karshe kan zaben da suka gabatar a Abuja, 'yan kallon suka ce an samu gazawa daga ita kanta hukumar zaben, ya zuwa ga masu takara, ko bayan tada hankalin da ya mamaye yakin neman zabe.

Masu sanya idanun na EU sun kara da cewa masu kada kuiri'a na Najeriya sun dawo daga rakiyar amfani da fasaha wajen kaiwa ga tabbatar da ingantaccen zaben sakamakon gazawa ta hukumar zaben na samar da sakamako nan take kamar yadda ta alkawarta. Sun fitar da wasu jerin batutuwa 23 da suka hada da wasu shida masu muhimmancin gaske da suka ce Najeirya na da bukatar kallo kan hanyar inganta tsarin zabe na kasar.

Barry Andrewas ya ce: "Yakin neman zabe ya zamo mai zafi, tare da mutunta tsarin taro domin yakin neman zaben, kamar yadda gangamin yakin neman zaben ya rika gudana a daukacin kasar. Sai dai an fuksanci kalubale irin na karancin Naira da na man fetur, da kuma tada hankalin da ya shafi yakin neman zaben a wasu wurare."

Nigeria Wahlen 2023
Lokacin da Atiku Abubakar na PDP ya kai wa sarkin Kano Aminu Ado Bayero ziyaraHoto: Sani Maikatanga/AP Photo/picture alliance

An yi amfani da addini da kabilanci a zabe

Sai dai sun nuna karfin ikon gwamnoni da amfani da kujerunsu ya karkatar da yakin neman zabe tare da jawo rabuwa bisa batun addini da kabila. Dama yakin zaben a bangaren masu takara ya jawo cikas daga rigingimu a tsakanin masu takara a cikin jam'iyyu. Masu sanya idanun sun lura da shari'u sama da 1000 kafin zabe da suka yi tasiri kan zaben. Ko bayan rigingimu sama da 100 da suka hada da asarar rai, wasu ayyukan 'yan laifi sun kawo cikas kan yakin neman zaben, ya kuma  shafi shi kansa zaben.

Duk da cewar rahoton mai shafi 92 ba shi da karfin yin tasiri bisa shari'un da ke gaban kotunan zabe na Najeriya, amma daga dukkan alamu bai zo ba da dadi ga ita kanta hukumar zabe ta kasar da ke ta kokarin wanke sunanta a kotunan da ma tsakanin al'ummar kasar,

Nigeria | Nach den Wahlen | Mahmood Yakubu
Shugaban INEC Yakubu Mahmood a lokacin da ya yi 'yan jarida bayani bayan zabeHoto: Kola Sulaimon/AFP/Getty Images

INEC ta nemi wanke kanta daga zargi

Festus Okoye da ke zaman kwamishina a hukumar zaben INEC ya ce sun yi rawar gani duk da jerin kalubale da suka fuskanta a yayin zaben. Ya ce " Ga batun zaben 'yan majalisar dattawa da na wakilai da zaben gwamnoni da na 'yan majalisar dokoki na jihohi, za ka gani cewar dukkanin 'yan kallo na cikin gida da na waje sun amince cewar akwai gagarumin ci-gaba kan yadda zaben ya gudana. Lallai akwai jerin kalubalen da ke tattare da shi, kuma in kana kallon wannan ya kamata ka kalli yanayin da aka yi zaben, da kuma muhallin zaben na batun rashin staro a sassan kasar. An rika kai hari kan ma'aikatanmu da ragowar al'umma ta kasa. Sannan kuma ga matsalar sake fasalin Naira. Mun kuma samu matsala ta jigilar kayan zabe.”