1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamfanin motocin Volkswagen zai biya diyya

Abdullahi Tanko Bala
May 26, 2020

Kotun kolin Jamus ta ce dole kamfanin motocin Volkswagen ya biya diyya ga wadanda suka sayi motocin da kamfanin ya yi kwangen tauye hayakin da suke fitarwa.

https://p.dw.com/p/3clEI
Autobranche in der Krise wegen Corona.
Hoto: picture-alliance/SvenSimon

Hukuncin ya bada dama ga wadanda suka gabatar da kara su mayar da motocin da suka saya wadanda aka yi kwange na tauye hayakin da suke fitarwa. 

Wadanda suka mayar da motocin za a biya su wani kaso na kudin da suka saya, sai dai kotun ta ce yawan kudin da za a mayar zai dogara ne da nisan tafiyar kilomitan da kowace mota ta ci tun bayan sayar da ita.

Hukuncin na daga tabargaza ta baya bayan nan da kamfanin motocin na Volkswagen ya tafka wanda aka bankado a shekarar 2015 yayin da aka gano ya yi kwangen tauye hayakin da motar ke fitarwa.

Hukuncin dai na iya yin tasiri akan wasu dubban kararraki da ke gaban shari'a wadanda ba a kammala su ba.