1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin harajin VAT ga tsarin federaliyyar Najeriya

September 9, 2021

A wani abun dake zaman zakaran gwajin dafi ga makomar tsarin federaliyyar tarrayar Najeriya, jihar Legas tabi sahun 'yar uwarta ta Rivers wajen kafa wata dokar harajin mai saye na VAT domin amfanin kansu.

https://p.dw.com/p/408Ts
Symbolbild Afrika Markt Bunt
Hoto: P. U. Ekpei/AFP/Getty Images

Jihohin biyu dai na zaman na kan gaba wajen tara harajin mai saye da ke zaman na biyu mafi tasiri a cikin tsarin harajin tarrayar Najeriya. Kuma a bisa al'ada hukumar tara haraji ta kasa FIRS ita ce karbar harajin sannan kuma ta sake rabawa a tsakanin matakan gwamnatin kasar guda uku kafin wannan sabon rikicin da a karkashinsa jihar Rivers da yar uwarta ta Legas dake zaman mafi bada gudunmawa ta harajin su yi gaban kansu wajen ayyana karbar harajin.

Nigeria Weihnachten Xmas
Hoto: DW/G. Hilse

Da ranar alhamis din nan ne dai majalisar dokokin Legas ta bi sahun yar uwarta ta Rivers wajen kafa dokar da ke jawo kace nace cikin kasar kuma ke zaman zakaran gwajin dafi ga makomar federalliyar tarrayar Najeriyar. Akwai dai tsoron matakin na iya kaiwa ga rusa tattalin arzikin akalla jihohi 30 da ke dogaro da harajin wajen biyan albashin ma'aikata da sauran bukatun yau da gobe. Barazanar kuma da a cewar Abubakar Ali dake zaman masanin tattalin arziki ke zaman mai girma.

Koma ta ina ragowar jihohin kasar ke shirin za su bi da nufin kaucewa barazanar mai tasiri, daga dukkan alamu kallo yana shirin komawa zauren majalisun kasar biyu inda hukumar tara harajin Najeriyar ta nufa domin neman sauki. FIRS dai na neman majalisun tarrayar da su kafa dokar da za ta bata kariya ta karbar harajin na mai saye ba tare da tsomin bakin jihohin ba.

Nigeria - Abuja tomato market
Hoto: DW/S.Olukoya

Ana dai kallon sabon matakin a matsayin sabuwar dabarar neman sauyin fasali a banagren jihohin kudu da suka dauki lokaci suna neman sauyin fasalin tafi da harkokin kasar amma kuma Abujar ta sa kafa ta na shurewa.

Sabon tsarin dai na nufin kara arziki a jihohi irin su Legas da fatakwal da ke samar da sama da kaso 70 cikin dari na harajin da kuma talauci da ke shirin mamaye ragowar talakawan da ke dogaro da harajin can baya.

Jihar Legas dai alal misali na tara abun da ya kai Naira miliyan dubu 500 ko kuma sama da kaso 50 cikin dari na daukacin harajin masarufin a daukacin kasar. To sai dai kuma a fadar Faruk BB Faruk da ke sharhi kan siyasar kasar sabuwar iskar da ke kadawa yanzu na zaman mai illa ga masu takama da arzikin dama talakawan tarrayar Najeriyar.

Abun jira a gani dai na zaman yadda za ta kaya a tsakanin masu ganin akwai alamun kaska a cikin auren zobe na kasar da kuma masu yi masa kallon mutu ka raba na takalmin kaza.