1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutum sama da 20 a hare-hare kan Kurdawa

Ramatu Garba Baba
November 20, 2022

Mutum akalla 27 sun mutu a yayin da wasu da dama suka jikkata a sakamakon wasu hare-hare ta sama da rundunar sojin Turkiyya ta kaddamar kan 'yan awaren PKK.

https://p.dw.com/p/4JneN
Jiragen yakin Turkiyya
Jiragen yakin TurkiyyaHoto: DHA/Demirören Nachrichten Agentur

Hare-hare da jiragin yakin sun salwantar da rayuka akalla ashirin da bakwai baya ga wasu fiye da talatin da aka ruga da su asibiti. Rundunar sojin Turkiyya ta kaddamar a hare-haren kan wasu sansanoni na mayakan Kurdawan PKK da ke kasashen Siriya da kuma Iraki, tare da lalata kayayyakin yakinsu, tana mai cewa, martani ne kan harin ta'addancin da suka kai wa kasarta a makon da ya gabata da ya kuma salwantar da rayukan mutane shida.

Gwamnatin Ankarar, ta sha zargin mayakan na PKK da laifin hana zaman lafiya a kasar ta kafin harin na makon jiya, inda ta sha alwashin ganin bayan 'yan awaren na Kurdawa da ta ce, sun addabi kasar da hare-haren ta'addanci da ke sanya fargaba a zukatan al'umma. Farmakin ya kasance mafi muni da Ankarar ta kai a baya-bayan nan kan mayakan na Kurdawa.