1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daukaka kara na tsohon firaminista

Suleiman Babayo AH/ATB
August 8, 2023

Tsohon Firaminista Imran Khan kasar Pakistan ya daukaka karar daurin shekaru uku da rabi da aka yanke masa kan tuhumar cin hanci da rasha.

https://p.dw.com/p/4Uuuc
Tsohon Firaminista Imran Khan na kasar Pakistan
Tsohon Firaminista Imran Khan na kasar PakistanHoto: Mohsin Raza/REUTERS

A wannan Talata tsohon Firaminista Imran Khan na kasar Pakistan ya daukaka kara kan hukuncin da aka yanke masa na daurin shekaru uku da rabi bisa tuhumar cin hanci da rashawa, kamar yadda lauya ya tabbatar.

Shi dai Khan kotu ta same da sayar da kayan da aka bashi kyauta lokacin da yake rike da madafun iko ba bisa ka'ida ba. Amma magoya bayan tsohon Firaminista Imran Khan na ganin duk abin da yake faruwa shafa kashin kaji ne daga gwamnatin Firaminista Shehbaz Sharif, abin da gwamnatin ta musanta.