1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tsananin zafi:Sudan ta Kudu ta rufe makarantun kasar

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
March 18, 2024

Ma'ikatun lafiya da na ilimin kasar sun shawarci iyaye da su killace 'ya'yansu a gida, kasancewar zafin zai kai mataki na 45 a ma'aunin Celcius, kuma duk makarantar da aka samu a bude to za a soke lasisinta

https://p.dw.com/p/4dpsH
Hoto: Samir Bol/ZUMAPRESS/picture alliance

Sudan ta Kudu ta sanar da rufe dukkan makarantun kasar sakamakon tsananin zafin da ake fuskanta, wanda hasashen masana yanayi ya tabbatar da cewa zai kara kamari nan da makonni biyu masu zuwa.

Karin bayani:'Yan gudun hijira na rikici a Sudan ta Kudu

Ma'ikatun lafiya da na ilimin kasar sun shawarci iyaye da su killace 'ya'yansu a gida, kasancewar zafin zai kai mataki na 45 a ma'aunin Celcius, kuma duk makarantar da aka samu a bude daga Litinin din nan to za a soke lasisinta.

Karin bayani:Sabon rikici ya barke a Sudan ta Kudu

To sai dai sanarwar rufe makarantun ba ta yi karin hasken ko yaushe wa'adin rufewar zai kare ba, inda al'umma suka maraba da wannan mataki, amma sun yi fatan ganin an sanya lantarki a makarantun don samun damar sanya na'urorin sanyaya azuzuwan.