1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNa duniya

Mulkin mallaka ya sauya yanayin mulki a Togo

April 8, 2024

A cikin watan Yuli na 1884, an ɗaga tutuar ‘yan mulkin mallaka a karo na farko a nahiyar Afirka – ba a Tanzaniya ko Namibiya ba, a Togo. Wannan ‘yar ƙaramar keɓaɓɓiyar gudundumar mulkin mallaka ita ce ta zama Togoland.

https://p.dw.com/p/4eWzX
Mulkin mallaka na Jamus a Afirka
Mulkin mallaka na Jamus a AfirkaHoto: Comic Republic

Ta wace hanya mulkin mallaka ya sauya yanayin mulki a Togo na tsawon lokaci?

A cikin watan Yuli na 1884, an ɗaga tutuar ‘yan mulkin mallaka a karo na farko a nahiyar Afrika – ba a birnin Tanzaniya ko na Namibiya ba, a birnin Togo. Wannan ‘yar ƙaramar keɓaɓɓiyar gudundumar mulkin mallaka ita ce ta zama Togoland. Da yake mulkin mallakar da Jamus ta yi a yankin na tsawon shekaru 30, ya kasance cikin ruwan sanyi, idan aka kwatanta da sauran yankuna da Jamus ta yi wa mulkin mallaka, sai aka ɗaga matsayin Togoland ta zamo "gundumar mulkin mallaka abar misali”. Sai dai kuma wannan tatsuniya ce kawai da hukumomin mulkin mallaka na Jamus suka ƙirƙira don biyan buƙatunsu.

Ta yaya Ƙasar Togo ta zama Gundumar Mulkin Mallaka ta Jamus?

Turawa sun shafe ɗaruruwan shekaru suna harkokin kasuwanci a gaɓar Afrika Ta Yamma. Wannan yanki shi masu zana taswira suka fi sani da Gaɓar Bayi, kuma hadahadar bayi ta wanzu har cikin ƙarni na 19. Asalin mutanen yankin sun amfana da wannan harka ta cinikin bayi, don haka lokacin da Kwamishinan Mulkin Mallaka na Jamus, Gustav Nachtigal, ya sanya hannu a kan yarjejeniyar bayar da kariya da Sarkin ƙabilar Ewe, Sarki Mlapa na Uku a 1884, sai wannan yarjejeniya ta zama babbar barazana ga manyan ƙasar Togo, don haka suka dinga zawarcin ƙasashen Turawa daban-daban suna gwara kawunansu.

Turawan mulkin mallaka na Jamus a Togo
Turawan mulkin mallaka na Jamus a TogoHoto: akg-images/picture-alliance

Sai dai kuma a wannan karon, za a samu matsaya a kan Keɓaɓɓiyar Gundumar mulkin mallakan ta Jamus ta farko da ke Lome: domin Turawa masu zana taswirar sun karkasa Gaɓar Afrika Ta Yamma zuwa Gwalkwas mallakar Ingila, da Togoland mallakar Jamus da kuma Dahomey mallakar Faransa.

Shin cikin ruwan sanyi Jamus ta gudanar da mulkin mallaka?

A'a, duk kuwa da imanin da aka yi cewa mulkin mallakar Jamus yana da sassauci a Togo, fiye da wanda ta gudunar a yankin Gabashin Afrika (kamar a Tanzaniya da Burundi da Rwanda) da kuma Kudu Maso Yammacin Afrika.

Bayan samun iko a gaɓar yankin, sai ‘yan mulkin mallakar Jamus suka ƙaddamar da tafiye-tafiyen ciwo garuruwa da ƙarfin soja a cikin tsakiyar Afrika. Bayanai sun nuna cewa an gudanar da irin waɗannan tafiye-tafiye kusan sau 60 tsakanin shekara ta 1884 zuwa 1902.  

Wane dalili ya sa ake yi wa Togo laƙabi da "Gundumar Mulkin Mallaka abar misali”?

Baya ga wannan mummunar fahinta da ake da ita cewa an samu zaman lafiya a mulkin mallakar Togo, akwai kuma batun cewa Togo ita ce kaɗai ƙasar da Jamus ta yi wa mulkin mallaka da ta riƙe kanta da kanta ta fuskar tattalin arziƙi. Shi kansa wannan iƙiƙrin ma yana buƙatar a fito da shi fili: ta iya riƙe kanta ne a dalilin tana samar da kuɗi ga harkokin kasuwancin Jamus, wanda aka jingina shi a kan harkokin noman zalunci da aka yi na manya gonaki na zalunci. 

‘Yan mulkin mallakar Jamus sun shigo da katafaren aiki gona inda ake noma amfanin gona kamar su kofi da auduga da koko da sauransu. Domin a samar da amfanin da za a sayar, an tursasa wa mutanen yankin wajen yin noma a manyan gonaki ana biyansu ‘yan kuɗi kaɗan, wani lokaci ma ba a biyansu. Yawancin amfanin da aka samu fitar da shi ake yi, kuma ribar da ake ci tana zaunawa ne a hannun Jamusawa. Daɗin munin abin ma shi ne, mahukuntan mulkin mallaka sun ƙaƙaba wa ƙananan manoma haraji.

Mahukunta ‘yan mulkin mallaka ba su zuba wani jarin kirki ba a kan kiwon lafiya da walwalar waɗannan ma'aikata ‘yan Togo ba, ko kuma a kan hanyoyi da gine-gine. Ƙwararru sun yi nuni da cewa game da haƙƙin bil'adama kuma, munin abin a ƙasar Togo ya kai yadda yake a sauran yankuna da Jamus ta mallaka, ga kuma nuna wariyar launin fata, da ƙazamin hukunci, da danniya da hukunta duk wanda ya yi adawa da mulkinsu. 

Ta wace hanya ‘yan mulkin mallaka suka yi tasiri a tsarin shugabanci na yankin?

Tun daga kafuwar ƙasar Togo a matsayin gundumar mulkin mallakar, iyakokinta ba sa wakiltar haƙiƙanin yadda yankin da mutanen wurin suke zaune ko cuɗanya da juna tun asali. Kuma har yau ɗin nan abin haka yake a taswira, inda za a ga Gana da Togo da Benin suna bakin gaɓa, inda suka miƙa suka shiga har cikin tsakiyar Afrika ta yamma, kamar an yanka kek kai-tsaye.  

Katin taswirar yamamcin Afirka a shekarar 1020
Taswirar yamamcin Afirka a shekarar 1020Hoto: The Print Collector/Heritage Images/picture alliance

A bisa dogaro da waɗansu jami'an sojan Jamus ‘yan ƙalilan da baƙin sojojin haya ‘yan Afrika, mahukuntan mulkin mallaka sun aikata cin zarafi da gangan, da murƙushe adawa da kuma maye gurbin tsarin mulkin gargajiya da sarakunan da suke yi musu biyayya. 

A zahirin gaskiya ma dai, wannan kalma ta "Shugaban ƙabila” babu ita a tsarin sarautun gargajiya na Togo, wanda yawancin waɗanda suke yin wannan sarauta jinin sarauta ne. A maimakon haka, sai aka naɗa "shugabanin ƙabilu” don su zama ‘yan koren mahukuntan mulkin mallaka, ba tare da la'akari da ainihin matsayinsu ba a cikin a'ummar Togo. A wajen yawancin ‘yan Togo, wannan kalma ta "Shugaban Ƙabila” kalma ce ta ƙasƙanci, domin kuwa muƙami ne da aka ƙirƙire shi don ya kare mutuncin ‘yan mulkin mallaka. Sarakunan gargajiya ba su da alhakin kula da gudanar da mulki ko tsarin gudanar da shi – a maimakon haka, matsayinsu da suke kai shi ne na siyasa da addini da, matsayin da ‘yan mulkin mallaka suka kasa fahinta ko kuma suka yi biris da shi. ‘Yan mulkin mallaka sun yi kuskure wajen ɗaukar cewa masinjoji ko kuma wakilai suna da wani ƙarfin iko, a maimakon ƙarfin ikon waɗanda suka aiko su, sannan kuma sai suka mara wa wakilan baya da ƙarfin mulkin mallaka. 

Rusa tsarin mulkin gargajiya, duk da rashin ingancinsa, ya zauna fiye da zamanin mulkin mallakar Jamus ko Faransa, kuma har yau ɗin nan ana ganin ɓurɓushinsa a gwagwarmayar neman mulki a cikin al'ummar Togo. 

Me ya faru da kasar Togo bayyana Jamusawa sun tafi?

Bayan da aka murƙushe Jamus a Yaƙin Duniya na 1, an raba ƙasar Togo tsakanin Faransa da Birtaniya. Mulkin mallakar Faransa da na Birtaniya, duk da farfagandar da aka dinga yaɗawa cewa ba haka ba ne, bai kyautata rayuwar talakan Togo ba. An shigar da Yammacin Togo cikin Gana, sannan kuma an ba wa ɗaya ɓangaren na Togo da Faransa ta mulka ‘yancin mulkin kai a 1960. Ƙabilu kamar su Ewe, waɗanda fasalin waɗannan iyakoki ya raba tsakaninsu, sun kai ƙara a kan wannan rabon da aka yi, har ma wasu daga cikinsu suna neman a yanka musu sabuwar ƙasarsu. Sai dai kuma har yau ɗin nan, waɗannan iyakoki da Faransa da Birtaniya suka yi yarjejeniya a kansu, sunan daram.