1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Atiku da Wike sun gaza cimma matsaya

Ubale Musa ZUD/AS
August 26, 2022

Duk da murnar da wasu 'yan jam'iyyar PDP suka fara yi a game da ganawar Atiku da Wike, akwai fargabar rashin samun fahimtar juna kan wasu sharuda da Gwamna Wike ya gindaya da watakila Atiku ba zai iya amincewa da su ba.

https://p.dw.com/p/4G7A0
Nigeria I Atiku Abubakar I PDP
Hoto: Uwais Abubakar Idris

Tattaunawa dai ta yi nisa a cikin jam'iyyar PDP ta adawa, inda dan takararta a zaben na badi Atiku Abubakar ya sauko daga dokin girma, ya fara lallashin mutumin da ya kayar a zaben fitar da gwani Nyesom Wike. Duk da cewar dai tattaunawar ta Atiku da Wike na gudana cikin sirri, matakin na shirin burge da dama a cikin jam'iyyar PDP ta adawa. Jagaba Adams Jagaba dai na zaman jigon jam'iyyar da kuma ya ce sabo na matakin na shirin tabbatar da nasarar yan Lemar a babban zaben na badi.

A yayin da Atiku ke neman goyon bayan Wiken, masu goyon baya na Wiken dai sun dage bisa bukatar saukar shugaban jam'iyyar PDP, kasa da wata guda a fara yakin neman zaben, matakin da rahotanni suka ce Atiku ya ce ba ta shirin sabuwa— wai bindiga a ruwa

Dan takarar sanata a jihar Kaduna Khalid Ibrahim da ke cikin magoya bayan Atiku a cikin jam'iyyarsu ta PDP ya ce Atikun zai iya lashe ko da kuwa babu goyon bayan Gwamna Wike.

Jam'iyyu na son cin ribar rikicin Atiku da Wike

Kawo yanzu dai ana zargin Gwamna Wiken na jihar Rivers da kokarin komawa bakin ganga da ke ta zaki ta ko'ina. Ko bayan tattaunawa ta Atikun, an hango Wiken na ganawa da dan takara na jam'iyyar Labour Party Peter Obi a karkashi na jagoranci na tsohon shugaban Najeriyar Olusegun Obasanjo.

Su kansu masu goya baya ga dan takarar shugaban kasa na APC Bola Ahmed Tinubu dai sun shaida wa DW cewa  Wiken ya amince ya yi aiki tare da su a wani abun da ke shirin jawo rudani a tsakanin na bangarorin guda uku. Wannan ta sanya mai sharhi kan harkokin siyasa Faruk BB Faruk cewa matakin ka iya lalata dimukuradiyyar Najeriya da ake ta kokarin ganin ta bunkasa.

APC ma na kokarin dinke barakar cikin gida

Majiyoyi a cikin jam'iyyar APC mai mulki ma dai sun ce Tinubu ya fara wani sabon yunkuri na lallashin 'yan jam'iyyar da suka fusata bayan zaben fitar da gwanin da aka kammala a watannin baya. Kama daga mataimaki na shugaban kasar Yemi Osinbajo ya zuwa ga tsohon ministan sufuri Rotimi Ameachi da ma shi kansa shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Ahmad Lawan sun zura wa dan takarar jam'iyyarsu Tinubu ido kan shirin yakin neman zabe, inda wasu ke cewa  sun koma 'yan kallo.