1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Yahouza Sadissou Madobi

August 27, 2013

Takaitaccen tarihin sabon Mnistan Sadarwa na Jamhuriyar Nijar

https://p.dw.com/p/19V8W
Yahouza SadissouHoto: DW

An haifi Yahouza Sadissou Madobi a shekarar 1966 a garin Madobi dake cikin Jamhuriyar Nijar. Kuma ya shafe shekaru kimanin 10 yana aiki a nan Sashen Hausa na DW.

Tsohon malamin makaranta ne. Ya zama dan majalisa cikin Jamhuriya ta Shida, kafin sojoji su kifar da gwamnatin a shekara ta 2010.

Ranar Talata 13 ga watan Agusta 2013 aka bayyana Yahouza Sadissou Madobi a matsayin Minsitan Sadarwa da hulda tsakanin hukumomin gwamnatin Nijar, a cikin sabuwar gwamnatin kasar da ta kunshi ministoci 36, karkashin Firaminista Briji Rafini.

Sai a saurari sautin da ke tare da wannan rubutu, domin jin cikakken hira da Yahouza bisa tarihinsa, wuraren da ya yi makaranta, da aiyuka kafin ya zama minista.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal