1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taliban na bikin cika shekaru biyu a mulki

Mouhamadou Awal Balarabe
August 15, 2023

Tutocin kasar sun ta kadawa a shingayen binciken a Kabul babbar birnin Afghanistan domin raya ranar da 'yan Taliban suka yi nasarar kafa gwamnatin Musulunci a kasar.

https://p.dw.com/p/4VCF1
Mayakn Taliban na muryar cika shekaru biyu da fara mulki a AfghanistanHoto: Ali Khara/REUTERS

Gwamnatin Taliban ta gudanar da bikin cika shekaru biyu da karbe mulki a Afganistan tare da mayar da kasar karkashin tsauraran dokokin Islama, matakin da kasashe da dama na duniya ke suka. Tutocin kasar sun ta kadawa a shingayen binciken na Kabul babban birnin kasar, domin tunawa da ranar da gwamnatin da ke samun goyon bayan kasashen yammacin duniya ta fadi tare da maye gurbinta da ta 'yan Taliban.

Sanarwar da hukumomin Afghanistan suka fitar ta bayyana ranar 15 ga watan Agustan shekarar 2021 a matsayin ranar nasara da ta share fagen kafa gwamnatin Musulunci a kasar. Sanarwar ta kara de cewa, kwace birnin Kabul shekaru biyu da suka gabata ya nuna cewa babu wata kasa ta ketare da za ta iya sake yi wa Afghanistan katsalandan.

Ita dai gwamnatin Taliban ta dauki tsauraran matakan addinin Musulunci musamman a kan mata tun bayan da ta hau kan karagar mulki, matakin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a matsayin nuna wariyar jinsi.