1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taiwan ta ce ba za ta mika wuya ga China ba

Binta Aliyu Zurmi
May 20, 2023

Shugabar kasar Taiwan Tsai Ing-wen ta sha alwashin ci gaba da samar da zaman lafiya a daukacin yankunan tsibirin duk kuwa da matsin lambar da suke fuskanta daga sojojin kasar China.

https://p.dw.com/p/4RbT8
Taiwan, Taipeh | Präsidentin Tsai Ing-wen am 7. Jahrestag ihrer Amtsübernahme
Hoto: Taiwan Presidential Office/Handout/REUTERS

Shugaba Ing-Wen ta bayyana cewar yaki ba shi ne mafita ba a yayin jawabinta na cika shekaruu 7 a kan karagar mulki, ka zalika ta ce ba za ta taba amincewa da Taiwan a matsayin wani bangare na kasar China ba kamar yadda suke ayyanawa.

Shugabar da ta lashi takobi, ta ce har ya zuwa shekarar mai zuwa da al'ummar kasar za su fita rumfunan zabe ta kuma mika mulki ga sabuwar gwamnati ba za ta mika kai ga matsin lambar da China ke musu ba.

Amurka da sauran kasashen yamma sun jima suna kokarin ganin sun taimaka wa tsibirin Taiwan wajen ci gaba da cin gashin kanshi, amma China ta ce ko da tsiya sai ta mayar da tsibirin karkashin ikonta.