1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ba ta kashin sojoji da 'yan ta'adda

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 24, 2021

Rahotanni da ke fitowa daga rundunar hadin gwiwa da ke sintiri a yankin Tafkin Chadi, na nuni da cewa ani ba ta kashi tsakanin jami'an tsaro da 'yan ta'adda.

https://p.dw.com/p/44oZG
Chad I Boko Haram
Yankin Tafkin Chadi na fama da barazanar 'yan ta'addaHoto: Jerome Delay/AP/picture alliance

Rundunar ta bayyana ba ta kashin a matsayin wanda suka yi nasara, ganin cewa sun halaka 'yan ta'addan har 22, koda yake suma a nasu bangaren suka yi asarar sojoji sida. Rundunar sojojin sama ta hadaka tsakanin Najeriya da Nijar ne dai suka fafata da 'yan ta'adda, sai sun ce sun samu daga kawayensu na Amirka. Da ma dai yankin na Tafkin Chadi da ke kan iyakokin Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi, na fama da hare-haren 'yan ta'addan Boko Haram masu gwagwarmaya da makamai da suka addabi kasashen yankin baki daya.