1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSomaliya

Somaliya ta yi tir da yarjejeniyar Habasha da Somaliland

Mouhamadou Awal Balarabe
January 2, 2024

Gwamnatin Somaliya ta kira jakadanta da ke Habasha domin tattaunawa da nuna bacin ranta game da sabuwar yarjejeniyar da ke ba wa hukumomin Addis-Ababa damar amfani da tashar jiragen ruwa yankin Somaliland da ya balle.

https://p.dw.com/p/4anXK
Taswirar Somaliya da Somaliland
Taswirar Somaliya da Somaliland

A lokacin da yake mayar da martani a birnin Mogadishu kwana guda bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar tsakanin Habasha da somaliland, firaministan Somaliya Hamza Abdi Barre ya ce kasarsa za ta bi dukkan hanyar da doka ta tanada domin yin tir da abin da ya kira yarjejeniyRikici na ci gaba a yankin Somalilandar ba-zata da ke yin karar tsaye karar tsaye ga ikonta.

Karin bayanRikici na ci gaba a yankin Somalilandi: 

Wannan yarjejeniyar ne ta zo ne a daidai lokacin da Somaliya da Somaliland suka amince a makon da ya gabata da dawowa kan teburin tattaunawa don warware matsalolin da suka ki ci ya ki cinyewa, bayan shafe shekaru ana takun saka tsakanin sassa biyu. Amma kuma Somalilya na ci gaba da daukar Somaliland a matsayin wani bangare na kasar, saboda haka ne ta dauki wannan mataki a matsayin cin zarafi.

Karin bayaniAl'ummar kasar Somaliya na bukatar agajin gagawa.

Sai dai har ya zuwa yanzu hukumomin Habasha ba su ce uffan game da matakin da Somaliya ta dauka bayan yarjejeniyar da ta cimma da Somaliland ba.