1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China da Rasha za su yi atisaye

Abdourahamane Hassane
July 16, 2023

Ma'aikatar tsaron kasar China ta ce kasashen China da Rasha za su gudanar da atisayen soji na hadin gwiwa a tekun Japan.

https://p.dw.com/p/4Ty3I
Golf von Oman | Russland, China und Iran halten gemeinsame Marineübung ab
Hoto: Northern Fleet Press Service/TASS/dpa/picture alliance

Kasashen biyu masu kusan ra'ayi daya wadanda ke da muradin tunkarar manufofin Amurka, sun kara yin kusanci da juna, tun lokacin da Rasha ta mamaye Ukraine, wanda Beijing ta ki yin Allah wadai da mamayar. A halin da ake ciki ba a a bayyana jadawalin ayyukan ba, amma ma'aikatar tsaron Chinar, ta ce jiragen ruwanta sun bar tashar jiragen ruwa ta Qingdao domin isa wurin atisaye