1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojin Najeriya na galaba a kan 'yan bindiga

July 2, 2021

Bisa ga dukkanin alamu rundunar sojin Najeriya na samu gagarumar nasara a kan mayakan ISAWP da Boko Haram a shiyyar Arewa maso Gabas, inda wasu majiyoyi masu zaman kansu ke cewa sun halaka mayaka 100 a cikin makon daya.

https://p.dw.com/p/3vwv8
Nigeria Soldaten in Damboa
Hoto: Getty Images/AFP/S. Heunis

A kusan kullum a ‘yan kwanakin nan sojojin Najeriya na ayyana samun nasara kan mayakan Boko Haram inda bayan dakile hare-hare da suke kaiwa, sojojin na kuma halaka su gami da kwace motocin yaki da makamai da ma kame wasu da ransu.Ko a sanarwar da rundunar sojojin Najeriya ta fitar ta nunar da cewa ko a jiya sun halaka mayakan ISWAP da Boko hara sama da 30 a jihar Yobe da kuma wasu da dama a sassan jihar Borno, bayan da suka nufi kai hari kan muradan jami'an tsaro da gwamnati. Wannan dai na da alaka da sauyin salo da sojojin suka yi a wannan yaki karkashin rundunar da ke yaki da ta'addanci a Arewa maso gabashin Najeriya da ake kira Operation Hadin kai.

Kamerun Mora Armee Soldaten Anti Boko Haram 07/2014
Kayan aiki da sojoji suka samu sun taimaka wajen murkushe 'yan bindigaHoto: Reinnier Kaze/AFP/Getty Images

Tasirin wadannan nasarori da sojojin da ke amfani da jiragen yaki da kuma sojojin kasa ya bayyana a fili, inda aka samu saukin hare-hare da ake samu a sassan jihohin Borno da Yobe inda hare-haren a baya suka fi kamari. Haka kuma matafiya na jigila ba tare da fargabar da suke fama da ita a baya ba, inda mutane ke rage zaman zullumi saboda sintiri da sojojin ke yi a tsakanin garuruwansu. Malam Muhammad Umar wani mazaunin yankin da  a baya ke fama da tsanantar hare-haren mayakan ISWAP da Boko Haram, ya ce yanzu kam sai hamdala don kuwa sun fara samun nitsuwa.

Mansana tsaro irin Kwamrade Baffa Musa na ganin cewa ya kamata sojojin Najeriya su fadada aikinsu daga tare hare-hare zuwa kai wa mayakan hare-hare har inda suke. Sai dai a cewar masharhanta ya zama dole sojojin su yi dukkanin mai yiwuwa domin ganin nasarorin da aka samu sun dore, ba wai bayan kwanki biyu lamarin ya sake tabarbarewa ba.