1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Siyasa ba da gaba ba' a Jamhuriyar Nijar

Salissou Boukari
July 4, 2022

‘Yan adawa a Nijar sun ce za su yi adawa ta ci gaban kasa ba tashin hankali ba. Tuni ma dai dan takarar hamayya a zaben bara, Mahamane Ousmane ya dauki wurinsa a majalisa.

https://p.dw.com/p/4DdXX
Bildkombo I Wahlen Niger I Mohamed Bazoum und Mahamane Ousmane
Shugaba Mohamed Bazoum da madugun adawa Mahamane Ousman

A Jamhuriyar Nijar bayan dogon lokaci na kaurace wa sabbin mahakumtan kasar sakamakon rashin yarda tun bayan zaben da ya gabata na shugaban kasa, ‘yan adawar kasar sun ce za su yi adawa ta ci gaban kasa ba ta tashin hankali ba, dan takarar hamayya a zaben da ya gabata, Mahamane Ousmane ya dauki wurinsa a majalisar dokoki.

Batutuwa biyu ne dai a jere suka dauki hankalin al'umma daga bangaran 'yan adawar kasar ta Nijar a baya-bayan nan, inda na farko shi ne kasancewar Alhaji Mahamane Ousmane a majalisar dokoki wanda ake ganin hakan na da nasaba da jawabin da ya yi bayan karshen shari'ar da ya shigar ta zabe ta kare, inda ya ce ba zai taba yin siyasa ta tashin hankali b illa sai dai ya bi hanyoyin doka, sannan na biyu sai ga kakakin gamayyar jam'iyyun na adawa Kane Habibou Kadaure ya fito ya ce ya amince da Bazoum a matsayin shugaban kasa ganin a baya ba haka yake ba amma kuma ya ce duk da haka yana cikin adawa tsumbul.

Sai dai daga bangaran masu mulki ta bakin Sahanine Mahamadou na jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarayya, wannan mataki da Mahamane Ousmane ya dauka da ma wasu yan adawar kasar ta Nijar shi ne ya kamata a cikin dimukuradiyya tunda dole ne sai an samu masu rinjaye da wadanda aka rinjaya.

Ya zuwa yanzu dai abin da ya rage shi ne ko dukannin yan adawar na Nijar za su dauki akida guda su gama karfi da karfe tare da bin wannan akida ta tsohon shugaban kasar ta Nijar mahamane Ousmane ta ganin a nan gaba sun yi tsaye wajen neman hakkokin al'umma ta hanyar doka ba wai da rigima ba.