1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabanni sun shirya wa murkushe Boko Haram

Ubale Musa M. Ahiwa
November 29, 2022

Bayan share tsawon lokaci ana kai komo, shugabannin kasashen tafkin Chadi na shirin yunkurin karshe da nufin murkushe kungiyar ta'addar Boko Haram da ke addabarsu.

https://p.dw.com/p/4KFon
Hoto: AFP/Getty Images

Sama da dalar Amirka miliyan 200 ne dai aka kai ga batarwa, ko bayan dubban sojoji a cikin yankin tafkin Chadi, duk dai a cikin neman kai karshen matsalar Boko Haram. To sai dai kuma shugabannin kasashen yankin sun ce sun fara ganin haske a kokari na kai karshen annobar zuwa gidan tarihi. Wajen wani taro na kasashen yankin guda shida a Abuja dai, shugabannin da suke fadin sun sha karfin kungiyar dai sun ce ana bukatar turin karshe da nufin kare ayyuka na Boko Haram a daukaci na tafkin Chadi.

Shugaba Buhari da ke jagorantar kungiyar kasashen yankin dai ya ce a shirye masu siyasar suke da su ba da daukaci na bukata da nufin sare kan macijin da ke ta shure-shure. Duk da cewar dai akwai alamun juyuwar reshe a cikin yakin da ke kallon karuwar cin dunun masu ta'addar, daga dukkan alamu akwai jan aiki a tsakanin jami'an tsaron da kaiwa ya zuwa kare ayyuka na kungiyar da ke tashi da lafawa yanzu.

Der nigerianische Präsident Buhari besucht den Bundesstaat Borno
Hoto: Bayo Omoboriowo

Ko a cikin makon da ya shude alal ga misali, ‘ya'yan kungiyar ISWAP sun yi nasarar hallaka sojojin Chadi kusan 40. To sai dai kuma a fadar Ambasada Mamman Nuhu da ke zaman shugaban hukumar gudanarwar tafkin Chadin, ana samun gagarumin ci gaba a kokari na kare ayyuka na kungiyar ta Boko Haram.

Karancina kudi game da matsalar isassun kayan aiki da ma bambanci na tunani a bangaren sojoji na kasashen yankin dai, na zaman babbar matsala da ke tarnaki ga samun nasarar sake tabbatar da zaman lafiya a cikin kasashen. Kafin sabon umurnin da a cewar Manjo Janar Abdul Khalifa Ibrahim da ke jagorantar sojoji na hadin gwiwar tafkin Chadin ke shirin sauya da dama a cikin yakin.

Sama da mutane miliyan 30 ne dai ke rayuwa a tafkin Chadin da ke zaman daya a cikin mafi girma a nahiyar Afirka kafin janyewa da kafewar da ta haifar da sauyin yanayi da ma rigingimu na rayuwa a cikinsa.