1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bayyana sakamakon zaben Saliyo

Suleiman Babayo LMJ
June 27, 2023

Hukumar zaben kasar Saliyo da ke yankin yammacin Afirka ta bayyana Shugaba Julius Maada Bio na kasar a matsayin wanda ya lashe zaben da ya gabata inda ya samu sabon wa'adi na shekaru biyar.

https://p.dw.com/p/4T8GW
Saliyo | Zabe | Julius Maada Bio
Shugaba Julius Maada Bio na SaliyoHoto: JOHN WESSELS/AFP/Getty Images

Hukumar zaben Saliyo ta bayyana Shugaba Julius Maada Bio, na jam'iyyar SLPP mai shekaru 59 a matsayin wanda ya lashen zaben da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata. Shugaba Bio ya samu kashi 56 cikin 100 na kuri'un da aka kada abin da ya tabbatar da cewa ya kaucewa tafiya zagaye na biyu na zabe da jagoran 'yan adawa Samura Kamara mai shekaru 72 da haihuwa na jam'iyyar APC wanda yake matsayi na biyu da kashi 41 cikin 100 na kuri'un.

Tun farko babbar jam'iyyar adawa ta kasar APC ta yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasar na wucin gadi, inda 'yan adawa suka yi zargin tafka magudi. Ana zaman tankiya tun bayan zaben da Shugaba Bio ya fafata da sauran 'yan takara 12.

Ita dai kasar Saliyo da ke yankin yammacin Afirka a baya ta yi fama da matsalolin annobar cutar Ebola a shekara ta 2014 sannan ta fuskanci yakin basasa tsakanin 1991 zuwa shekara ta 2002 inda fiye da mutane 50,000 suka halaka.