1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Bama ya sha alwashin kare Musulmin kasar

May 6, 2013

Akalla mutane 200 aka kashe tare da kona dubban gidaje abin da ya tilasta tashin mutane dubu 140 daukaci Musulmin Rohingya sakamakon wani rikici a jihar Rakhine dake yammacibn kasar.

https://p.dw.com/p/18TBE
Myanmar President Thein Sein delivers a speech at the United Nations during the Economic and Social Commision for Asia and the Pacific (ESCAP) 69th Session of the Commission in Bangkok on April 29, 2013. ESCAP is held from 25 April to 1 May in Bangkok. AFP PHOTO/ Nicolas ASFOURI (Photo credit should read NICOLAS ASFOURI/AFP/Getty Images)
Hoto: Nicolas Asfouri/AFP/Getty Images

Shugaban kasar Bama ko Myanmar Thein Sein ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta yi dukkan abin da ya kamata domin ganin ta kare hakkin Musulmin dake zaune a kasar da mabiya addinin Budha ke da rinjaye.

Thein Sein ya bada wannan tabbacin ne yayin da ake tsaka da fargabar fadan na addini ka iya ci-gaba da watsuwa, bayan da ya kai dab da babban birnin kasar wato Yangon a makon daya gabata.

Shugaban kasar ya kuma bukaci alu'mma da su gujewa gaba yana mai cewa wasu mutane ne suka yi amfani da damar fadar albarkacin baki da suke da ita ta hanyar da ba ta dace ba tare da rura wutar rikicin addini a kasar.

Thein Sein ya kara da cewa gwamnatainsa za ta yi aiki da shawarwarin da kwamitin da gwamnatin ta kafa domin gudanar da bincike kan rikicin addinin a Jahar Rakhine dake yammacin kasar.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal